APC ta Ƙara Tumbatsa, Ta Karbi Shugabannin Jam'iyyar PDP da Mutane Sama da 500

APC ta Ƙara Tumbatsa, Ta Karbi Shugabannin Jam'iyyar PDP da Mutane Sama da 500

  • Jam'iyyar APC ta ƙara samun ƙarfi bayan daruruwan mutane daga jam'iyyun adawa sun koma cikinta a jihar Abia da ke Kudu
  • Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 500 ne daga jam'iyyun PDP, LP YPP da AFGA suka fice suka koma APC cikin mako guda
  • Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Hon. Benjamin Kalu ne ya karbi mutanen yayin wata ziyara da ya kai a mazabarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Abia - Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Hon. Benjamin Kalu ya karbi daruruwan mutane da suka sauya sheka daga jam'iyyun adawa zuwa APC a Abia.

Benjamin Kalu ya fara ziyarce ziyarce zuwa mazabarsa ne tun ranar 3 ga watan Agusta domin yin godiya bisa zaɓensa da aka yi.

Kara karanta wannan

'Za mu dawo': APC ta tsure, matasan da suka kona sakatariya sun tura sakon barazana

Benjamin Kalu
APC ta karbi wanda suka sauya sheka a Abia. Hoto: Rep. Benjamin Okezie Kalu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa jami'in yada labaran Benjamin Kalu, Levinus Nwabughiogu ne ya sanar da lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane 500 sun koma APC a Abia

Levinus Nwabughiogu ya ce a lissafin da suka yi mutane akalla 500 ne suka dawo APC a mazabar Bende da ke jihar Abia.

Ya kuma bayyana cewa mutanen sun hada da shugabannin jam'iyyun PDP, LP AFGA YPP da magoya bayansu.

Levinus Nwabughiogu ya kara da cewa mutanen sun bayyana cewa amincewa da jagorancin Benjamin Kalu ne yasa suka sauya shekar.

Ben Kalu ya karbi mutane zuwa APC

Vanguard ta wallafa cewa Hon. Benjamin Kalu ya karbi mutanen da suka sauya sheka wajen mika musu tsinsiya da ke nuna alamar jam'iyyar.

A ziyarce ziyarcen da Benjamin Kalu ya yi ya ziyarci akalla mazabu 13 tun fara ziyarar da ya yi a ranar 3 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Ana kuka da APC, Ganduje ya dafe jiga jigan PDP, sun daukarwa jam'iyya alkawari

Ziyarar da Kalu ya fara ta samu tarba daga manyan yan siyasa a jihar Abia inda suka yaba masa bisa kokarin da ta yi a shekara daya.

Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Edo

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi babban kamu yayin da jiga-jigan jam'iyyar PDP suka sauya sheka.

Rahotanni na nuni da cewa jiga-jigan jam'iyyar sun watsar da PDP ne inda APC musu tarba nai kyau a birnin Benin City da ke Kudancin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng