Rikici Ya Barke, PDP Ta Dakatar da Tsohon Gwamna a Arewa, Ta Jero Dalilai

Rikici Ya Barke, PDP Ta Dakatar da Tsohon Gwamna a Arewa, Ta Jero Dalilai

  • Jam'iyyar PDP ta dauki muhimmin mataki bayan ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom
  • PDP ta dakatar da tsohon gwamnan ne kan zargin cin dunduniyarta musamman a tarurrukan jam'iyyar
  • Ortom na daga cikin kungiyar G5 inda suka goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2023 madadin Atiku Abubakar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Jam'iyyar PDP a jihar Benue ta dakatar da tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom.

Jam'iyyar ta dauki mataki ne saboda zargin Ortom da yi mata zagon kasa yayin taron jam'iyyar da aka yi.

Jam'iyyar PDP ta dakatar da tsohon gwamna a Najeirya
Jam'iyyar PDP ta dakatar da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom. Hoto: @SamuelOrtom.
Asali: Twitter

PDP ta dakatar da tsohon gwamna, Ortom

TheCable ta tattaro cewa PDP na zargin Ortom da kawo rudani yayin taron jam'iyyar na unguwanni da kuma satar kayayyakin zabe.

Kara karanta wannan

Ana cikin kushe mulkin APC, dan takarar shugaban kasa a PDP ya dawo jami'yyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta ce halayyar Ortom ta cin dunduniyar jam'iyyar ta hana samun damar gudanar da tarurruka a kananan hukumomin jihar da dama.

Sauran wadanda aka dakatar a PDP

An dakatar da Ortom ne har na tsawon wata daya tare da wasu mutane guda uku da ake zarginsu tare, cewar Punch.

Sakataren jam'iyyar a jihar, Joseph Nyam shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a jiya Litinin 5 ga watan Agustan 2024.

"Yayin gudanar da tarurrukan jam'iyyar PDP a ranar 27 ga watan Yulin 2024 a unguwanni 276, ka kawo rudani wurin goyon bayan satar kayayyakin zabe."
"Hakan ya jawo rashin gudanar da tarurrukan a kananan hukumomin Buruku da Gboko da Ushongo da Guma da Tarka da Rwande da kuma Ohimini."

- Joseph Nyam

Ortom na cikin kungiyar G5 a PDP

Ortom ya kasance na hannun daman Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda suka fandare a lokacin zaben shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da zanga-zanga a Najeriya, gobara ta kama a kamfanin NNPCL

Tsofaffin gwamnonin PDP da suka hada da Samuel Ortom da Nyesom Wike da Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu sun goyawa Bola Tinubu baya a zaben 2023.

Sai kuma gwamnan mai ci na jiyar Oyo, Seyi Makinde shi ma yana daga cikin gwamnonin da ake kira G5.

Dan takarar shugaban kasa ya koma APC

Kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi babban kamu bayan tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP ya watsar da jami'yyarsa.

Mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Kalu shi ya karbi tsohon dan takarar mai suna Dakta Cosmos Ndukwe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.