Gwamnan PDP da Kansa Ya Yabawa Tsarin Tinubu, Ya Roki ’Yan Jiharsa a Arewa
- Yayin da ake cigaba da zanga-zanga a Najeriya, Gwamna Ahmadu Fintiri ya roki al'ummar jihar Adamawa
- Gwaman ya yi musu godiya kan gudanar da zanga-zanga ba tare da ta da tarzoma ba inda ya ce an ji kokensu
- Fintiri ya tabbatar musu da cewa Bola Tinubu shugaba ne mai jin koken al'ummarsa kuma zai dauki mataki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya roki al'ummar jihar kan zanga-zanga da ake yi.
Fintiri ya ce Shugaba Bola Tinubu mutum ne mai jin koken jama'a inda ya ce zai shawo kan matsalolin kasar.
Zanga-zanga: Finitiri ya yabawa tsarin Bola Tinubu
Gwamnan ya bayyana haka yayin jawabi ga 'yan jihar a yau Lahadi 4 ga watan Agustan 2024, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fintiri ya bukaci al'umma da su zauna lafiya da juna inda ya yaba musu kan yadda suka gudanar da zanga-zanga a jihar.
"Za mu yi aiki da ku domin tabbatar da an shawo ka bukatunku da kuke da su."
"Shugaba Bola Tinubu mutum ne mai jin koken jama'a kuma zai kawo karshen matsalolin kasar."
- Ahmadu Fintiri
Zanga-zanga: Fintiri ya yabawa al'ummar jihar Adamawa
Fintiri ya ce yana alfahari da 'yan jihar saboda yadda suka gudanar da zanga-zanga a kwanaki hudu cikin kwanciyar hankali.
Gwamnan ya kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya yi mai yiwuwa wurin kawo karshen bukatun 'yan kasar.
Ya ce zamna lafiya ne kadai zai ba gwamnati damar gudanar da ayuukan cigaba a jihar.
Tinubu ya magantu kan tallafin mai
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan dawo da tallafin man fetur da ya jefa al'umma cikin kunci a Najeriya.
Tinubu ya ce babu ranar dawo da tallafin saboda an cire shi ne saboda inganta tattalin arzikin kasar da ke cikin matsi.
Shugaban ya ce cire tallafin ya zama dole duk da ya san halin kunci da hakan ya jefa 'yan Najeriya a ciki na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng