Saraki Ya Musanta Ikirarin Tambuwal Kan Janyewa Atiku a Zaben Fidda Gwani, Ya Fadi Dalilai

Saraki Ya Musanta Ikirarin Tambuwal Kan Janyewa Atiku a Zaben Fidda Gwani, Ya Fadi Dalilai

  • Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya musanta ikirarin Aminu Tambuwa yayin zaben fidda gwanin PDP
  • Saraki ya ce Tambuwal ya dauki matakin janyewa Atiku Abubakar a zaben fidda gwanin 2022 ba tare da sanar da su ba
  • Ya ce kwata-kwata ba shi da shirin janyewa wani dan takara saboda haka ba ya cikin shirin Tambuwal ko matakin da ya dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Tsohon gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki ya yi magana kan ikirarin Aminu Waziri Tambuwal a zaben fidda gwanin PDP.

Saraki ya musanta cewa Tambuwal ya sanar da shi zai janyewa Atiku Abubakar a zaben fidda gwani da aka yi kafin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Bayan gwamna a Arewa ya ki albashin N70,000, NLC ta fadi matakin da za ta dauka

Saraki ya yi martani ga Tambuwal kan janyewa Atiku a zaben fidda gwani
Bukola Saraki ya musanta Tambuwal kan janyewa Atiku a zaben fidda gwanin shugaban kasa. Hoto: @Tambuwal_101/@ORderPaper/@atiku.
Asali: Twitter

Atiku: Saraki ya yi martani ga Tambuwal

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Yusuph Olaniyonu ya fitar, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Saraki na zuwa ne bayan Tambuwal ya yi magana a hirarsa da Arise TV inda ya ce bai san da lamarin ba, Vanguard ta tattaro.

Saraki ya ce ya yi mamaki da maganan inda ya ce bai taba tsammani ba kawai ya ga Tambuwal ya janyewa Atiku a zaben fidda gwanin 2022 na shugaban kasa.

Saraki ya fayyace gaskiya kan ikirarin Tambuwal

"Ina son fayyace abin da ya faru bayan Tambuwal ya yi magana da daliget tare da janyewa Atiku Abubakar inda ya bukaci a goya masa baya."
"Duk da yake Tambuwal abokina ne amma bai sanar da ni hakan ba kafin ya yanke hukunci."

Kara karanta wannan

"Ku rike gwamnoninku": Minista ya tona abin alheri da Tinubu ya yi wa jihohi

"Ba ni da masaniya kan abin da ya aikata ko kuma shawarar da ya yanke kuma ba ni da shirin janye takara ga Atiku."

- Bukola Saraki

Bagudu ya yi magana kan albashinsa

Kun ji cewa Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya yi magana kan zargin facaka da suke yi a gwamnati.

Bagudu ya ce kwata-kwata mota daya yake shiga a hukumance inda ya bayyana cewa albashinsa ko miliyan daya bai kai ba.

Tsohon gwamnan Kebbi ya ce bai san da wani alawus da Minista ke karba ba idan ba albashinsa ba da ya ke samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.