PDP Ta Fadi Musabbabin Rashin Yin Zanga Zanga a Zamfara, Ta Jero Dalilai

PDP Ta Fadi Musabbabin Rashin Yin Zanga Zanga a Zamfara, Ta Jero Dalilai

  • Yayin da ake cigaba da zanga-zanga a Najeriya, jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta yabawa Gwamna Dauda Lawal kan shugabanci
  • Jam'iyyar ta ce salon mulkin Lawal Dare shi ne musabbabin rashin gudanar da zanga-zanga da aka yi a sauran jihohi
  • Shugaban riko na jam'iyyar a jihar, Mukhtar Lugga shi ya tabbatar da haka inda ya ce 'yan Zamfara suna cikin farin ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta bayyana dalilin da ya hana gudanar da zanga-zanga da ake gudanarwa.

PDP ta ce zanga-zangar ba ta samu damar isa jihar ba da ke Arewa maso Yammacin kasar saboda shugabanci nagari.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Tinubu sun yi kishiyar zanga zanga a Kano, su na goyon bayan gwamnati

PDP ta yabawa salon mulkin Dauda Lawal a Zamfara
Jam'iyyar PDP a Zamfara ta yabawa salon mulkin Gwamna Dauda Lawal. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Facebook

Zamfara: PDP ta fadi dalilin kin hawa tituna

Mukaddashin shugaban jam'iyyar, Mukhtar Lugga shi ya bayyana haka a jiya Juma'a 2 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukhtar ya ce irin salon shugabancin Gwamna Dauda Lawal shi ne musabbabin rashin gudanar da zanga-zangar a jihar.

Ya ce 'yan jihar Zamfara suna murna da salon shugabancin Dauda Lawal inda ya ce an cimma abubuwan cigaba da dama, Tribune ta tattaro.

Zamfara: PDP ta yabawa mulkin Dauda Lawal

"Mazauna jihar Zamfara suna cikin farin ciki da murna kan salon shugabanci a jihar da abubuwan da aka samu na cigaba."
"Gwamnati ta samar da wasu tsare-tsare da kuma shirye-shirye masu muhimmanci da za su taimaki al'ummar jihar."
"Gwamnan ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimi da kuma lafiya wanda ya yi matukar tasiri wurin sauya al'amura."

Kara karanta wannan

Ana fargabar miyagu za su shiga zanga zanga, an samu hanyoyi 5 domin kare kai

- Mukhtar Lugga

Sanata ta musanta hannu a zanga-zanga

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ireti Kingibe ta yi martani bayan zarginta da hannu a cikin zanga-zangar da ake yi a Najeriya.

Sanata Kingibe ta musanta labarin inda ta ce wani tsohon bidiyo ne ake yadawa da ya kai kimanin makwanni shida da daukarsa.

Wannan na zuwa ne bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce jami'an tsaro sun gano Sanata da ke daukar nauyin zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.