Gwamna Ya Zargi Wasu Manyan Ƴan Siyasa da Hannu a Rura Wutar Zanga Zanga

Gwamna Ya Zargi Wasu Manyan Ƴan Siyasa da Hannu a Rura Wutar Zanga Zanga

  • Malam Uba Sani ya zargi wasu ƴan adawa da suka sha kaye a zaɓen 2023 da hannu a zanga-zangar yunwa da ake yi a ƙasar nan
  • Gwamnan jihar Kaduna ya ce ƴan adawa na amfani da zanga-zangar da zummar ɗaukar fansa kan kashin da suka sha a zaɓe
  • Kalaman Uba Sani na zuwa ne yayin da ƴan Najeriya suka shiga rana ta biyu da fara zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati mai ci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi zargin cewa ‘yan adawa na amfani da zanga-zangar da ake yi domin daukar fansar kashin da suka sha a zaɓen 2023.

Gwamnan ya yi iƙirarin cewa wasu ƴan adawa ne ke tunzura matasa da sauran talakawa su shiga wannan zanga-zanga da aka fara ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

"Arziki da talauci duk na Allah ne," Gwamna a Arewa ya yiwa masu zanga zanga nasiha

Gwamna Uba Sani.
Gwamna Uba Sani na Kaduna ya zargi wasu ƴan adawa da hannu a zanga-zanga Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Malam Uba Sani ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin Channels tv mai taken, "zanga-zangar watan Agusta," ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya faɗawa ƴan adawa mafita

Uba Sani ya yi kira ga ire-iren waɗannan ƴan adawar da su jira babban zaɓe na gaba sannan su nuna karfinsu a gaban akwatun zaɓe.

Gwamnan ya caccaki wasu jagororin zanga-zangar waɗanda ya yi zargin cewa sun bar ta a hannun ƙananan yara masu karamin tunani maimakon su jagorance su.

Ya tuna lokacin da yake matashi ɗan gwagwarmaya a zamanin mulkin soji, yana mai cewa ya jagoranci zanga-zangar adawa da karfa-karfar sojoji amma ya ƙare a gidan yari.

Gwamnan Kaduna ya hana APC ɗaukar mataki

Gwamna Sani ya ƙara da cewa wasu daga cikin ƴaƴan APC sun nemi ya bari su shirya zanga-zangar adawa da masu wannan zanga-zanga amma ya hana su.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanya dokar zaman gida ta awanni 24, ya tsara yadda za a yi Sallar Jumu'a

A cewarsa, ya hana su ne saboda mutunta ƴancin zanga-zanga da kowa ke da shi kuma shi kansa ya yi amfani da ƴancinsa a zamanin mulkin sojoji.

A ƙarshe, Gwamnan Kaduna ya buƙaci ƴan Najeriya su kara ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu lokaci domin farfaɗo da tattalin arziki, rahoton The Cable.

Sanusi II ya koka kan zanga-zanga

Kuna da labarin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayyana illar da zanga-zanga ta haifar a jihar da Arewacin Najeriya.

Sanusi II ya ce tun farko wannan tashin-tashinar malamai da shugabanni su ke gudu shiyasa suka yi ta kashedin a gujewa zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262