An Ɗage Zanga Zangar da Matasa Za Su Fara Yau a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana
- A yau Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024 matasan Najeriya suka shirya fita zanga-zanga domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa
- Sai dai wata sanarwa da ta bayyana da yammacin jiya Laraba, ta yi iƙirarin cewa masu shirya zanga-zangar sun ɗaga ta zuwa watan Oktoba
- Fitaccen ɗan gwagwarmaya kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake ganin su ne gaba a shirya zanga-zangar, Omoyele Sowore ya mayar da martani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ikeja, jihar Lagos - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya musanta rahoton ɗaga zanga-zangar yunwa da za a fara yau Alhamis.
Sowore ya bayyana sanarwar da ke yawo cewa an sauya tsarin zanga-zangar a matsayin ƙarya mara tushe balle makama.
Ikirarin janye zanga-zanga daga Agusta
Legit Hausa ta fahimci cewa wata takarda ɗauke da sa hannun darektan shirye-shirye na ƙungiyar Take It Back Movement ta yi ikirarin cewa an canza ranar fara zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce "saboda rashin tsaro da ake fama da shi," masu shirya zanga-zanga "sun yanke shawara mai tsauri" na dage ta zuwa ranar 1 ga Oktoba.
Gwamnatin tarayya ta sha nanata cewa tana gudun abin da zai je ya dawo shiyasa take ƙara rokon ƴan Najeriya sun janye shirinsu na zanga-zanga.
Da gaske an ɗage zanga-zanga?
Da yake mayar da martani a shafinsa na X, Sowore ya bayyana cewa hadiman Tinubu ko jami'an tsaro na Abuja ne ke yunkurin lalata shirin ƴan Najeriya.
Sowore, ɗaya daga cikin waɗanda ake ganin su ke shirya zanga-zangar ya ce babu fashi, za a fara wannan zanga-zanga gobe (yau) Alhamis.
Haka nan kuma ƙungiyar Take It Back Movement ta musanta jita-jitar janye zanga-zanga.
Ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X cewa:
"Ku yi watsi da sanarwar, sun fara yaɗa farfaganda da karerayin da suka saba."
Fadar shugaban ƙasa ta tona asiri
A wani rahoton na daban, fadar shugaban ƙasa ta zargi wasu masu karfin faɗa aji a gwamnati da hannu a shirya zanga-zangar da za a fara yau Alhamis.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin ɗalibai, Sunday Asefon ne ya bayyana hakan a wani taro da aka shirya a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng