Ana Tunkarar Zanga Zanga, Sanata Ndume Ya Ja da Matakin Majalisar Dattawa

Ana Tunkarar Zanga Zanga, Sanata Ndume Ya Ja da Matakin Majalisar Dattawa

  • Sanata Muhammad Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya yi fatali da sabon ofishin da aka ba shi a majalisar dattawan Najeriya
  • A wata wasiƙa da ya tura ga majalisar, Ali Ndume ya ce ofishin da aka ba shi bai yi daidai da girmarsa a majalisar tarayyar ba
  • Wannan dai na zuwa ne bayan majalisar ta sauke shi daga matsayin mai tsawatarwa saboda ya soki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammad Ali Ndume, ya yi watsi da sabon ofishin da kwamitin ayyuka na majalisar dattawa ya canza masa.

Ali Ndume ya sanar da ƙin karɓan sabon ofishin a wata wasiƙa da ya aike wa kwamitin ranar Talata, 30 ga watan Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Majalisar Dattawa ta sanar da mutuwar fitaccen sanatan APC

Sanata Muhammad Ali Ndume.
Sanata Ndume ya yi fatali da sabon ofishin da majalisa ta ba shi Hoto: Muhammad Ali Ndume
Asali: UGC

Ya bayyana cewa sabon ofishin da aka ba shi ya ƙasƙantar da shi idan aka duba girmansa da ƙimarsa a majalisar dattawa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Ndume ya ƙi karɓan sabon ofis

Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun sakataren Ndume, Yati Shuaibu Gawu, ta ce:

"An umurce ni da in sanar da ku cewa mai girma Sanata Mohammed All Ndume, bai amince da sabon ofishi mai lamba 3.10 da kwamitin ya ba shi ba.
"Ya ɗauki wannan matakin ne saboda a bisa al'adar majalisar dattawa ana raba ofisoshi ne daidai da girma da daɗewa a majalisa.
"Sanata Ndume shi ne Sanata mafi daɗewa bayan Sanata Ahmad Lawan kuma zai karɓi ofis ne kawai a hawa na hudu."

Meyasa aka canza wa Ndume ofis?

Idan ba ku manta ba a kwanakin baya majalisar dattawata sauke Ali Ndume daga matsayin mai tsawatarwa na majalisa saboda suka da ya yi wa gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu: Wasu bayanai sun fito bayan majalisa ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi

Wannan dalilin ne ya sa kwamitin kula da ayyukan majalisar ya sauya masa ofis, wanda kuma ya ce ba zai karba ba saboda ba girmansa ba ne, Tribune Nigeria ta rahoto.

Sanata Akpabio ya kira taron gaggawa

A wani rahoton kuma, an ji Sanata Godswill Akpabio ya katse hutun majalisar dattawa, ya kira taron gaggawa kan muhimmin batun da ya shafi ƙasa baki ɗaya.

Magatakardar majalisar dattawa, Chinedu Akubueze ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya aike wa sanatoci ranar Litinin, 29 ga watan Yuli 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262