Jigon APC Ya Fasa Kwai, Ya Fallasa Masu Daukan Nauyin Zanga Zanga

Jigon APC Ya Fasa Kwai, Ya Fallasa Masu Daukan Nauyin Zanga Zanga

  • Jagororin jam'iyyar APC na kara daukan zafi kan shirin matasan Najeriya na yin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a dukkan jihohi
  • Jigon APC a yankin kudu maso kudu, Dakta Blessing Agbomhere ya yi kira na musamman ga matasan Najeriya kan hakura da zanga zanga
  • Dakta Blessing Agbomhere ya kuma fallasa wadanda yake zargi da shirya zanga zangar domin kawo cikas ga gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Maganar zanga zangar adawa da tsadar rayuwa na Najeriya na cigaba da daukan hankulan jagororin jam'iyyar APC a Najeriya.

Shugaban tsare tsaren APC a kudu maso kudancin Najeriya, Dakta Blessing Agbomhere ya ambaci sunayen masu daukar nauyin zanga-zangar.

Kara karanta wannan

An gaida matasa: Muhimman nasarori 3 da barazanar zanga zanga ta samar ga talakawa

Bola tinubu
Jigon APC ya fallasa masu daukar nauyin zanga zanga. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Dakta Blessing Agbomhere ya ce dole ne a kara hakuri kafin abubuwa su daidaita a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Agbomhere kan masu daukar nauyin zanga zanga

Jigon APC a Kudu, Dakta Blessing Agbomhere ya ce fusattatun yan siyasa ne da suka fadi zabe ke zuga matasa fitowa zanga zanga.

Dakta Blessing Agbomhere ya ce nan gaba kadan za su wallafa sunayensu a duniya kowa ya gansu.

Agbomhere ya yi kira ga shugabanni

Vanguard ta wallafa cewa Dakta Blessing Agbomhere ya yi kira ga dukkan masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya da su rika ƙoƙarin ganin sun kawo sauyi a yankunansu.

Jigon jami'yyar APC ya ce dole sai an hada hannu wajen magance matsalolin Najeriya domin Bola Tinubu shi kadai ba zai iya kasancewa a ko ina ba.

Kiran jagoran na APC ga yan Najeriya

Kara karanta wannan

Kungiyar duniya ta goyi bayan 'yan zanga zanga a Najeriya, ta taso 'Yan majalisa a gaba

Haka zalika, jigon APC ya bayyana cewa kawo gyara a Najeriya ba abu mai sauki ne ba musamman yadda tattalin kasar ya rikice.

Saboda haka ya yi kira ga yan Najeriya kan kara hakuri har zuwa lokacin da mutane za su fara gani a kasa.

Zanga zanga: Yan sanda sun yi gargadi

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da matasa ke shirin fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya, yan sanda sun aika sako a Yobe.

Rundunar yan sandan jihar Yobe ta sanar da samun bayanan sirri kan yadda Boko Haram ke kokarin shiga cikin matasan su kawo tarzoma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng