Zanga Zanga: Matasa Sun Ki Jin Bari, APC Ta Fadi Babban Matakin da Za Ta Dauka

Zanga Zanga: Matasa Sun Ki Jin Bari, APC Ta Fadi Babban Matakin da Za Ta Dauka

  • Shugabannin jam'iyyar APC na jihohi sun sanar da fara tattakin nuna goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Za a fara tattakin ne daga ranar 29 ga yuli zuwa 11 ga Agustan 2024 kuma 'ya 'yan jam'iyyar za su yi gangami a fadin kasar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da babbar zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Tinubu kan tsadar rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam'iyyar APC ta sha alwashin tattara 'ya 'yanta tun daga matakin gunduma, kananan hukumomi da jihohi domin gudanar da gangami.

Shugabannin jam'iyyar APC na jihohi sun ce za su fara gudanar da gangamin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu daga 29 ga Yuli zuwa 11 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: APC ta yi zargin juyin mulki ga Tinubu, ta fadi matakin da za ta dauka

APC ta yi shirya gudanar da gangamin nuna goyon baya ga gwamnatin Tinubu
Shugabannnin APC na jihohi sun sanar da gangamin nuna goyon baya ga Bola Tinubu. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Kungiyar shugabannin jam’iyyar APC ta jihohi sun bukaci masu shirin yin zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Tinubu da su yi watsi da wannan shiri, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za ayi zanga-zangar adawa da Tinubu

Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan Najeriya musamman matasa sun ce za su fara gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu daga 1 zuwa 10 ga Agusta.

Masu shirya zanga-zanga sun ce hakan ya zama dole ne biyo bayan yadda lamuran tattalin arziki suka tabarbare a karkashin Shugaba Tinubu yayin da talaka ke shan wuya.

Sai dai shugabannin jam’iyyar APC na jihohin sun ce rahotannin tsaro sun bankado shirin da wasu ‘yan adawa ke yi na hambarar da gwamnatin Tinubu ta hanyar zanga-zangar.

APC za ta gudanar da gangamin kasa

Jaridar Punch ta ruwaito sakataren kungiyar kuma shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Cross River, Alphonsus Ogar Eba ya ce:

Kara karanta wannan

Fargabar zanga zanga: Ganduje ya gana da ciyamomi APC a jihohi, bayanai sun fito

"Daga ranar 29 ga watan Yuli zuwa 11 ga watan Agusta 2024 za mu fara gudanar da gangamin nuna goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
"Za mu gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna godiya ga irin ayyukan raya kasa da kuma shirye-shiryen da Shugaba Tinubu ya kawo da suka tabbatar da dimokuradiyya.
"Muna kira ga dukkanin 'ya'yan jam'iyyarmu da ma 'yan Najeriya masu kishi da su zo mu yi wannan gangami domin shaidawa duniya cewa gwamnatin Tinubu na kokari."

Minista ya nemi alfamar 'yan Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa karamin ministan albarkatun ruwa, Bello Goronyo, ya roki wadanda suka shirya zanga-zangar yunwa da su janye matakin da suka dauka.

Barista Bello Goronyo ya bayyana cewa bai kamata a fara yiwa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu hisabi daga yin shekara daya a mulki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.