Zanga zanga: APC Ta Yi Zargin Juyin Mulki Ga Tinubu, Ta Fadi Matakin da Za Ta Dauka

Zanga zanga: APC Ta Yi Zargin Juyin Mulki Ga Tinubu, Ta Fadi Matakin da Za Ta Dauka

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shirya domin fara zanga zangar nuna goyon baya ga shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Sakataren kungiyar shugabannin APC na jihohi, Alphonsus Ogar Eba ne ya bayyana haka a yau Litinin a birnin tarayya Abuja
  • Alphonsus Ogar Eba ya bayyana cewa dole su tashi domin dakile yunkurin kawo cikas ga mulkin demokradiyya a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta yi gargadi kan yunkurin juyin mulki ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Sakataren kungiyar shugabannin APC na jihohi 36, Alphonsus Ogar Eba ya ce akwai mummunar manufa a cikin zanga zangar da ake shirin yi.

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Rukunin mutane 3 da suka juyawa Abba Gida Gida da NNPP baya a watan nan

Tutar APC
APC ta yi zargin yaki da dimokuradiyya a lokacin zanga zanga. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa APC za ta yi zanga zangar nuna goyon baya ga Bola Tinubu a dukkan jihohin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC: 'Juyin mulki ko zanga zanga?'

Jami'yyar APC ta yi zargin cewa akwai masu manufar kifar da gwamnatin Bola Tinubu a cikin zanga zangar da ake shirin yi.

Sakataren kungiyar shugabannin APC na jihohi, Alphonsus Ogar Eba ya ce kifar da gwamnati ba abu ne mai kyau ga dimokuraɗiyya ba.

Matakin da jam'iyyar APC za ta dauka

Vanguard ta wallafa cewa Alphonsus Ogar Eba ya ce za su dauki matakin yin zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadin Najeriya.

Sakataren ya ce za su fito zanga zangar goyon bayan ne a tun ranar 29 ga watan Yuli har 11 ga watan Agusta.

APC ta yi kira ga yan Najeriya

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Matasa sun ki jin bari, shugabannin APC sun fadi matakin da za su dauka

Jam'iyyar APC ta yi kira ga yan Najeriya kan cewa ka da su yarda a musu barazana a cutar da su da sunan zanga zanga.

Haka zalika jami'yyar ta umurci yan Najeriya da su hada kai da jami'an tsaro wajen ganin an tona asirin masu shirin kawo tarzoma a Najeriya.

Zanga zanga ta barke a jihar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Neja na nuni da cewa matasa sun fara gudanar da zanga-zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Masu zanga zangar sun fito kan tituna ne dauke ta alluna suna rera wakokin da kira ga gwamnatin tarayya kan kawo saukin rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng