APC Ta Birkice Bayan Dakatar da Shugaban Jam'iyya da Sauran Shugabanni

APC Ta Birkice Bayan Dakatar da Shugaban Jam'iyya da Sauran Shugabanni

  • Jam'iyyar APC ta ɗauki matakin ladabtarwa kan shugabanta na jihar Enugu, Cif Ugochukwu Agballah
  • Kwamitin zartarwa na jam'iyyar a jihar ya dakatar da shugaban tare da wasu mambobin kwamitin daga kan muƙanmansu
  • Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar a jihar, ya bayyana cewa an dakatar da su bisa wasu zarge-zarge da ake yi musu da suka haɗa da cin dunduniyar jam'iyyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - Jam’iyyar APC reshen jihar Enugu ta dakatar da shugabanta, Cif Ugochukwu Agballah daga kan muƙaminsa.

Jam'iyyar ta kuma dakatar da wasu mambobin kwamitin zartaswa bisa wasu zarge-zargen da ake yi musu.

APC ta dakatar da shugabanta a Enugu
An dakatar da shugaban jam'iyyar APC a jihar Enugu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Sakataren yaɗa labaran APC a jihar, Cif Michael Ezeanyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban tare da sauran ƴan kwamitin zartarwar jam’iyyar na jiha a birnin Enugu ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

APC ta samu gagarumar matsala bayan manyan jagororinta 500 sun koma PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka dakatar da shugaban APC?

Ezeanyanwu ya bayyana cewa mambobin kwamitin zartarwa na jihar Enugu sun kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da ayyukansu saboda cin dunduniyar jam'iyyar da suka yi, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

"Mu ƴan kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC reshen jihar Enugu, mun kaɗa ƙuri’ar rashin amincewa da Cif Ugochukwu Agballah (shugaban jam'iyyar na jiha), Cif Augustine Alumonah (mataimakin shugaban jam'iyya na jiha)."
"Sauran sun haɗa da Mista Jude Aniogbo (ma’aji na jiha) da Mista Emeka Eze (sakataren tsare-tsare na jiha), sannan an dakatar da su daga jam’iyyar."
"Shawarar da muka yanke ta dogara ne a kan wasu ayyuka na cin mutuncin ofis, ƙwace ƙarfin iko, kawo rarrabuwar kai ta hanyar samar da ɓangarori da korar shugabannin jam’iyya ba bisa ƙa'ida ba."

- Cif Michael Ezeanyanwu

A cewar Ezeanyanwu, tun bayan tabbatar da Agballah a matsayin shugaban APC na jihar, ya ke gudanar da al’amuranta yadda ya ga dama ba tare da la’akari da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya sake yiwa PDP lahani, 'yan majalisa 3 sun koma APC

Karanta wasu labaran kan APC

Jagororin APC sun koma PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Cross Rivers ta samu koma baya bayan wasu manyan jagororinta sun koma jam'iyyar PDP.

Kimanin jagorori 500 na jam’iyyar APC a ƙananan hukumomi bakwai na mazaɓar Sanatan Cross Rivers ta Kudu suka tsallaka zuwa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng