Fargabar Zanga Zanga: Ganduje Ya Gana da Ciyamomi APC a Jihohi, Bayanai Sun Fito
- Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, jam'iyyar APC ta yi zama da shugabanninta a jihohi 36 da ke fadin kasar
- Shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje shi ya jagoranci ganawar a jiya Juma'a 26 ga watan Yulin 2024 a birnin Tarayya Abuja
- Yayin ganawar, an bukaci ciyamomin musamman a jihohin APC da su hada kai da gwamnoni domin shawo kan zanga-zangar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya yi wata ganawa da shugabannin APC a jihohi 36 a kasar.
Ganawar ba ta rasa nasaba da shirin zanga-zanga a fadin kasar da matasa suka shirya saboda mawuyacin hali da ake ciki.
Musabbabin ganawar Ganduje da ciyamomin APC
Sakataren jam'iyyar ta kasa, Felix Morka shi ya tabbatar da haka a jiya Juma'a 26 ga watan Yulin 2024, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje wanda ya jagoranci ganawar ya bukaci ciyamomin su zauna da gwamnonin jihohi musamman na APC domin dakile zanga-zangar.
Yayin ganawar, jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa ana shan wahala a kasar tare da nuna damuwa musamman irin halin da ake ciki.
Sakataren jam'iyyar ya ce akwai wadansu da ke son kawo rigima a zanga-zangar wadanda ba a san ko su waye ba ne, Daily Trust ta tattaro.
Zanga-zanga: Shawara da aka ba ciyamomin APC
"Yayin ganawar mun yi duba zuwa ga halin da ake ciki da kuma shirin zanga-zanga da za a fara a ranar 1 ga watan Agustan 2024."
"Tabbas ana cikin wani hali a Najeriya duk da haka muna tare da Bola Tinubu wurin shawo kan matalolin da ake fuskanta a kasar.
"Gwamnati tana iya bakin kokarinta wurin samar da sauki ga 'yan kasa yayin da wasu ke kokarin kawo rigima."
- Felix Morka
'Yan sanda sun gindaya sharuda ga masu zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta ba da damar yin zanga-zanga amma ta kasance cikin lumana ba tashin hankali.
Daga cikin sharudan shi ne shugabannin zanga-zangar su ba da bayanansu ga kwamishinonin 'yan sanda da ke jihohinsu daban-daban.
Asali: Legit.ng