Sanata Ali Ndume Ya Bayyana Gwamna 1 a Arewa da Ya Sa Zai Ci Gaba da Zama a APC

Sanata Ali Ndume Ya Bayyana Gwamna 1 a Arewa da Ya Sa Zai Ci Gaba da Zama a APC

  • Muhammad Ali Ndume ya bayyana dalilin da ya sa zai ci gaba da zama a jam'iyyar APC bayan sauke shi daga matsayinsa a majalisa
  • Yayin da ya karbi bakunci kungiyoyin mata a Maiduguri, Sanatan Kudancin Borno ya ce zai bi sawun duk inda Gwamna Zulum ya sa ƙafa
  • Wannan dai na zuwa ne bayan jam'iyyar APC ta buƙaci Ndume ya koma wata jam'iyyar adawa bayan sauke shi daga kujerar mai tsawatarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Muhammad Ali Ndume ya gindaya sharaɗin da zai riƙe shi a jam'iyyar APC mai mulki.

Sanata Ndume ya ce zai ci gaba da zama a APC matuƙar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum nan cikin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

Sanata Muhammad Ali Ndume.
Ali Ndume ya gindaya sharaɗin da zai ci gaba da zama a APC Hoto: Sen Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Ali Ndume ya rasa kujera a majalisa

Daily Trust ta ce Ali Ndume ya bayyana haka ne ranar Alhamis a gidansa da ke Maiduguri yayin da yake jawabi ga ƙungiyoyin magoya bayansa mata da suka kai masa ziyara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dandazon matan sun sha alwashin za su yi zanga-zanga a zauren majalisar tarayya tsirara domin nuna adawa da tuge Ndume daga matsayin mai tsawstarwa.

Idan ba ku manta ba majalisar dattawa ta sauke Ndume daga matsayinsa ne saboda sukar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Ndume: 'Dailin zama na a APC'

Da yake jawabi ga ƙungiyoyin matan, Sanata Ali Ndume ya ce:

"Dangane da kiran jam'iyyar APC ta kasa cewa na tattara na bar jam'iyyar zuwa wata, ina son tunatar da mu cewa Allah ne kaɗai ke bayar da mulki ga wanda ya so.

Kara karanta wannan

Tinubu na kokarin lallaba matasa, zanga zanga ta barke a Abuja kan tsige Ndume

"Saboda haka ina ƙara bayyana cewa ina ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC. Jagoranmu Gwamna Zulum yana cikin APC kuma duk inda ya sa ƙafa ni ma ina nan."

Ndume ya tabbatar da cewa matuƙar Gwamna Zulum bai bar APC ba, shi ma ba zai barta ba.

Akpabio ya nemi afuwar Sanata Natasha

A wani rahoton kun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya nemi afuwar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Godswill Akpabio ya nemi afuwar Sanatan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, kan wasu kalamai da ya furta mata a kwanakin baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262