"Za Mu Iya," Shugaban INEC Ya Yi Magana Kan Gudanar Zaben Kananan Hukumomi 774
- Hukumar INEC ta bayyana cewa za ta iya shirya zaɓukan ƙananan hukumomi a faɗin Najeriya idan aka ɗora mata nauyin hakan
- A yau Alhamis Farfesa Mahmud Yakubu ne ya faɗi haka a gaban kwamitin haɗin guiwa na majalisar tarayya mai kula da harkokin zaɓe
- Shugaban INEC ya ce idan ana bukatar hukumar ta ɗauki nauyin zaɓukan to dole sai an yi wa kundin tsarin mulkin ƙasa garambaul
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta iya gudanar da zaben kananan hukumomi cikin kwanciyar hankali idan aka ɗora mata alhakin hakan.
Shugaban hukumar INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli, 2024.
Mahmud Yakubu ya faɗi haka ne a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin haɗin guiwa na majalisar tarayya mai kula da harkokin zaɓe, kamar yadda The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar INEC ya gindaya sharaɗi
Ya ce INEC za ta iya gudanar da zabukan kananan hukumomi amma hakan zai yiwu ne kawai idan an yiwa doka garambawul don ba ta damar yin hakan.
Farfesa Mahmud ya yi nuni da cewa INEC ta dade tana gudanar da zaben ciyamomi a babban birnin tarayya cikin nasara ba tare da samun matsaloli ba.
INEC ta saba zaben kananan hukumomi
Shugaban ya ce tun da INEC take shirya zaɓen kananan hukumomin Abuja, ba a taba samun lokacin da jam'iyya ɗaya ta lashe dukkan kujeru ba, wanda a jihohi kuwa hakan ba sabon abu ba ne.
Mahmud Yakubu ya shaida wa ƴan majalisar cewa idan nauyin shirya zaɓen kananan hukumomi ya dawo ƙarƙashin INEC, zai zama alheri ga demokuraɗiyya.
Sai dai ya ce hakan za ta faru ne kaɗai idan an yi wa kundin tsarin mulki garambawuul domin karɓe nauyin zaben daga hannun jihohi, a maida karkashin INEC, rahoton Vanguard.
Kano za ta gudanar da zaɓen ciyamomi
A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta mutunta hukuncin kotun koli kan tabbatar wa kananan hukumomi 'yancin gashin kansu.
Darakta Janar kan yada labaran gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya kara da cewa gwamnati ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng