Zanga Zangar Adawa da Tinubu: Jam'iyyar APC Ta Dauki Muhimmin Mataki
- Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun nuna damuwarsu kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a ranar 1 ga Agustan 2024
- Jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta gayyaci shugabanninta na jihohi domin gudanar da wani taron gaggawa
- Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar na ƙasa ya yi kira ga ƴan Najeriya da su haƙura da zanga-zangar tare da hawa kan teburin sulhu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta gayyaci shugabanninta na jihohi domin yin taro kan zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a faɗin ƙasar nan.
Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru ne ya bayyana hakan bayan taron kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) karo na 153 da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja.
APC ta buƙaci a janye zanga-zanga
Sanata Ajibola Basiru ya ce kwamitin NWC ya bi sahun shugaban ƙasa wajen yin kira ga masu shirin zanga-zangar da su janye shirinsu, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun bukaci ƴan Najeriya da su yi amanna cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta magance halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Kwamitin na NWC ya kuma yi kira ga iyaye da su sa ido kan motsin ƴaƴansu domin hana wasu su ɗauki hayarsu domin tayar da rigima gabanin zanga-zangar da aka shirya a ranar 1 ga watan Agusta.
"Taron ya buƙaci dukkanin masu shirya zanga-zangar da su aminta da ƙoƙarin da shugaban ƙasa ke yi na sake farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa, tare da tabbatarwa ƴan Najeriya cewa nan ba daɗewa ba ko zuwa gaba kaɗan za a shawo kan ƙalubalen.
"Kwamitin na NWC ya kuma kira taron gaggawa na shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 36 na tarayya domin ci gaba da tattaunawa."
- Sanata Ajibola Basiru
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Gwamnatin Tinubu ta bayyana dalilin da ya sa ba ta son a yi zanga zanga
- Gwamnatin Tinubu ta fadi hanyar magance zanga zangar da ake shirin yi
- Kungiyar kwadago ta janye shiga zanga-zangar adawa da Tinubu? Gaskiya ta bayyana
Jigon APC ya ba da shawara ga matasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon jam’iyyar APC a jihar Ondo, Dakta Femi Adekanmbi, ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan.
Jigon na APC ya yi kira ga matasan Najeriya da su janye zanga-zangar da suke shirin yi a fadin ƙasar nan saboda halin ƙuncin da ake ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng