Tsohon Kakakin Kamfen PDP Ya Mayar da Zazzafan Martani ga Atiku kan Zanga Zanga

Tsohon Kakakin Kamfen PDP Ya Mayar da Zazzafan Martani ga Atiku kan Zanga Zanga

  • Daniel Bwala ya caccaki tsohon mai gidansa Atiku Abubakar kan zanga-zangar da matasa ke shirin gudanarwa a watan Agusta
  • Tsohon kakakin kamfen Atiku ya ce zanga-zangar ba ta zama dole ba domin shugaban ƙasa na iya bakin ƙoƙarinsa wajen yayewa ƴan Najeriya damuwa
  • Bwala ya bayyana haka ne a fadar shugaban ƙasa jim kaɗan bayan ganawa da Bola Ahmed Tinubu ranar Laraba, 24 ga watan Yuli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okiwa a zaben 2023, Daniel Bwala, ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Bwala, wanda ya sanar da ficewa daga PDP a hukumance, ya soki Atiku bisa nuna goyon bayan zanga-zangar da matasan Najeriya ke shirin yi a watan Agusta.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

Atiku Abubakar, Daniel Bwala da Bola Tinubu.
Tsohon kakakin kamfen PDP ya soki kalaman Atiku da ke nuna goyon baya ga zanga-zangar matasa Hoto: @Atiku, @BwalaDaniel
Asali: Twitter

Channels tv ta tattaro cewa Daniel Bwala ya mayar da wannan martani ne yayin hira da ƴan jarida a fadar shugaban kasa bayan ganawa da Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana zanga-zangar da ƴan Najeriya suka shirya yi ta tsawon kwana 10 a matsayin makircin siyasa.

Mista Bwala ya ce ya kamata ƴan adawa sun jingine siyasa, su taho su haɗa kai da shugaban ƙasa a ƙoƙarinsa na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan.

Bwala a aika saƙo ga ƴan Najeriya

Haka nan kuma ya buƙaci ƴan Najeriya da su karawa Shugaba Tinubu lokaci domin cimma kyawawan manufofinsa ga Najeriya.

A cewarsa, shugaban ƙasa yana sane da kuncin rayuwar da ake ciki kuma zai yi iya bakin ƙoƙarinsa domin share hawayen ƴan ƙasa, rahoton Daily Trust.

"Na yi farin cikin ganawa da shugaban kasa a yau domin nuna goyon bayana gare shi kan namijin kokarin da yake yi na warware matsalolin da ke addabar ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu: Fitaccen Sarki ya aika muhimmin saƙo ga matasa masu shirin yin zanga zanga

“Mai girma shugaban kasa ya damu da halin da mutane ke ciki kuma yana bakin kokarinsa wajen yaye masu duka abubuwan da ke damunsu,” in ji shi.

Sai dai duk da haka ya amince da ƴancin gudanar da zanga-zamgar lumana amma a cewarsa da wuya zanga-zanga ta kasa baki ɗaya ta ƙare lafiya.

Gwamnoni sun sa labule a Abuja

A wani rahoton kun ji cewa gwamnonin Najeriya ƙarƙashin kungiyar NGF sun shiga taro na musamman a daidai lokacin da matasa ke shirin yin zanga-zanga.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnonin na gudanar da taron sirri a sakatariyar NGF da ke birnin Abuja kuma ana sa ran za su tattauna kan abubuwa uku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262