Sauya Sheka: Cikakken Jerin Sunayen Sanatocin Labour Party da Suka Rage a Majalisar Dattawa
Abuja - A tarihi, ana ganin cewa jam’iyyar Labour (LP) ta sha fafutukar kwatar kanta daga rinjayen jam’iyyu masu karfi irin APC da PDP a siyasar Najeriya.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sai dai LP ta samu gagarumin ci gaba a Mayun 2022 lokacin da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi ya shige ta, inda ya jawo dumbin magoya baya musamman matasa.
Tasirin Peter Obi ya taimaka wajen karawa jam’iyyar dama a siyasar Najeriya. Yanzu dai Labour tana da sanatoci biyar a zauren majalisar dokokin kasar.
Jam'iyyar Labour Party ta gamu da cikas
Duk da wannan ci gaban, jam’iyyar ta samu koma baya a jiya Talata bayan da Sanata Ezenwa Onyewuchi ya sauya sheka zuwa APC, inda ya bar Labour da sanatoci biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mun ruwaito cewa an sanar da ficewar Onyewuchi a majalisar dattawa, inda sajan din majalisar dattawa ya umarce shi da ya hau sabuwar kujera a cikin ‘yan majalisar masu rinjaye.
Ga jerin sanatocin jam’iyyar Labour a kasa:
Okechukwu Ezea – Mazabar Enugu ta Arewa
An haifi Okechukwu Ezra a jihar Enug ga Theresa da James Ezea. Ya yi karatun firamare da sakandare a Makarantar Al'umma da ke Umachi, da kuma Nsukka.
Ezra ya yi karatu mai zurfi a jami’ar Najeriya da ke Nsukka, inda ya kammala digirinsa na biyu a fannin kimiyyar siyasa a shekarar 1986. Ya kuma samu digiri na LL.B da LL.M a fannin shari’a a Jami’ar Legas, Akoka.
Ireti Kingibe – Sanatar birnin Abuja
An haifi Ireti Heebah Kingibe a ranar 2 ga Yuni, 1954, a jihar Kano. Injiniya ce kuma ’yar siyasa da aka zabe ta matsayin sanatar Abuja a zaben 2023 karkashin jam’iyyar Labour.
Kingibe ta fito daga wani fitaccen gida, kasancewar kanwa ce ga Ajoke Muhammed, matar tsohon shugaban Najeriya Murtala Muhammed.
Neda Imasuen – Mazabar Edo ta Kudu
Neda Bernards Imasuen sanata daga Edo, wanda aka zaba a shekarar 2023 domin wakiltar mazabar Edo ta Kudu a majalisar dattawan kasar karkashin Labour.
Imasuen ya samu shaidar zama lauyan kotun koli ta Najeriya a shekarar 1985 sannan ya sami digiri na biyu a fannin harkokin gwamnati daga jami'ar Long Island a shekarar 2004.
Victor Umeh – Sanatan Anambra ta tsakiya
Victor C. Umeh dan siyasa ne wanda ya taba rike mukamin shugaban jam’iyyar APGA ta kasa, kuma a halin yanzu Sanata ne mai wakiltar Anambra ta tsakiya karkashin Labour.
An haifi Umeh a ranar 19 ga Yuli, 1962, a Aguluzigbo, karamar hukumar Anaocha ta Anambra, ga dangin Kirista. Ya samu nasarori a harkokin siyasa, inda ya rike mukamai daban-daban.
Tony Nwoye – Mazabar Anambra ta Arewa
Tony Okechukwu Nwoye shi ne sanatan Anambra ta Arewa a karkashin jam'iyyar Labour.
Kafin ya zama sanata, ya kasance dan takarar gwamna a jihar Anambra a karkashin jam'iyyar PDP a 2013 da kuma APC a 2017.
Peter Obi ya fadi sharuddan hadaka
A wani labarin, mun ruwaito cewa jagoran jam'iyyar Labour, Peter Obi ya bayyana wasu sharudda da za a cika idan ana so ya shiga hadakar jam'iyyun da za su yaki APC a 2027.
Peter Obi ya ce matuƙar aka samu daidaito kan yadda za a magance matsalolin Najeriya a tsakaninsu zai goyi bayan haɗakar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng