Tinubu Ya Sha Kakkausar Suka Daga Gida, Jigon Siyasar PDP Ya Tono Babban Kuskurensa a Mulki
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya zargi shugaba Bola Tinubu da tafka babban kuskure
- Dele Momodu ya bayyana cewa Bola Tinubu ya yiwa Najeriya kallon jihar Legas ne da ya mulka a shekaru da suka gabata
- Haka zalika Dele Momodu ya yi magana kan irin ministocin da shugaba Bola Tinubu ya zabo domin su taya shi aiki a gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya kara suka ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Dele Momodu ya ce al'amura sun rikice a Najeriya karkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Dele Momodu ya dora laifi ga Tinubu kan cewa ya yiwa Najeriya kallon jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin rikicewar mulkin Bola Tinubu
Dele Momodu ya yi ikirarin cewa Bola Tinubu ya dauko irin tsarin jihar Legas ne na 1999 zuwa 2007 ya kawo shi a Najeriya.
Jaridar the Cable ta wallafa cewa saboda haka ne Dele Momodu ya ce dole lamura ba za su tafi yadda ya kamata a mulkinsa ba.
Momodu: 'Ba kwararru a mulkin Tinubu'
Dele Momodu ya yi ikirarin cewa cikin abin da ya hana lamura tafiya akwai rashin aiki da mutane da suke da kwarewa da Tinubu yake yi.
Ya ce duk cikin ministocin Bola Tinubu ba zai iya samun mutum 10 da suke da kwarewa a fannoni ba kafin a ba su matsayi.
Ana nuna wariya a Najeriya
Dele Momodu ya kara komawa da kan cewa akwai mutane kwararru da ya kamata a rika damawa da su amma an ki a zakulosu.
Ya ce hakan kuma na faruwa ne saboda yadda ake nuna wariya da wadanda ba 'ya'yan manya ba a kasar.
Ahmed Lawan ya ba Tinubu shawara
A wani rahoton, kun ji cewa a yayin da al'ummar Najeriya ke kara shiga kuncin rayuwa saboda tsadar kayayyaki, Sanata ya tura sako ga Bola Tinubu.
Sanata Ahmed Lawan daga jihar Yobe ya bayyana halin da ake ciki a Najeriya da kuma abin da ya kamata shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng