Matasa Na Shirin Yin Zanga Zanga, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Matasa Na Shirin Yin Zanga Zanga, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Ɗan majalisar wakilai daga jihar Kogi, Hon. Salman Idris ya sauya sheƙa daga ADC zuwa jam'iyyar APC ranar Talata, 21 ga watan Yuli
  • Kakakin majalisar wakilai, Rt Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙar sauya sheƙar da ɗan majalisar ya miƙa masa a zaman yau a Abuja
  • Salman ya bayyana cewa rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar ADC ta ƙasa ne dalilinsa na sauya sheka zuwa APC mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Kogi, Salman Idris ya sauya sheƙa daga jam'iyyar ADC zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulkin Najeriya.

Honorabul Salman, mai wakiltar mazaɓar Kabba-Bunu/Ijumu a majalisar wakilai ta ƙasa ya fice daga ADC zuwa APC yau Talata, 23 ga watan Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki mataki kan kudirin sabon mafi karancin albashi da Tinubu ya mika

Hon Salman Idris.
Dan majalisar wakilai daga jihar Kogi, Salman Idris ya koma jam'iyyar APC Hoto: @OWealthcome
Asali: Twitter

A rahoton Daily Trust, ɗan majalisar ya sanar da sauya sheka ne a wata wasika da kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya karanta a zaman yau Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan Imo ya koma jam'iyyar APC

Wannan na zuwa ne mintuna kaɗan bayan ɓullar labarin cewa sanata mai wakiltar Imo ta Gabas a inuwar Laboour Party, Ezenwa Onyewuchi ya koma APC.

Hakan na kunshe a wata wasiƙar sauya sheƙa da shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya karanta a zaman sanatoci na yau Talata a Abuja.

Jaridar The Cable ta tattaro cewa Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo kuma shugaban gwamnonin APC na cikin zauren majalisar a lokacin da aka karanta saƙon.

Meyasa Hon Salman ya koma APC?

A nasa ɓangaren, ɗan majalisar Kabba-Bunu/Ijumu, Salman Idris ya bayyana cewa ya ɗauki matakin komawa APC ne saboda rigingimun cikin gida da suka addabi jam'iyyar da ya baro ADC.

Kara karanta wannan

Ganduje ya gurgunta shirin Obi, sanatan jam'iyyar Labour ya sauya sheka zuwa APC

Ya ce ya yanke shawarin haɗewa da APC mai mulki bayan tattaunawa da al'ummar mazaɓarsa da sauran masu ruwa da tsaki.

APC ta fara zawarcin gwamnan PDP

A wani rahoton kuma jam'iyyar APC ta fara zawarcin Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Masu ruwa da tsakin APC a shiyyar sun fara tuntuɓa da zaman tattaunawa kan yadda za su jawo gwamnan daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262