Sanata Ndume Ya Yi Magana Kan Batun Zanga Zangar Matasa, Ya Kawo Mafita 1

Sanata Ndume Ya Yi Magana Kan Batun Zanga Zangar Matasa, Ya Kawo Mafita 1

  • Yayin da matasa ke shirin zanga-zanga a wata mai kamawa, Sanata Ali Ndume ya bai wa shugaban Bola Tinubu mafita
  • Sanata Ndume mai wakiltar Kudancin Borno ya bukaci Tinubu ya kira masu shirya zanga-zangar su zauna a teburin sulhu
  • Wannan kalamai na zuwa ne bayan kungiyar kwadago NLC ta ba Tinubu shawarar ya saurari koken matasan da ke shirya zanga zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sanata Muhammad Ali Ndume ya shawarci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bi ta lalama da tattaunawa wajen magance zanga-zangar da matasa ke shirin yi.

Ali Ndume ya ba shugaban ƙasa wannan shawarar da yake ganin ita ce mafita ranar Litinin gabanin zanga-zangar wadda matasa suka tsara yi ranar 1 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 10 ayi zanga zanga, Tinubu ya dawo Najeriya bayan kammala taron AU

Bola Tinubu da Ali Ndume.
Sanata Ali Ndume ya shawarci Shugaba Tinubu ya zauna da masu shirya zanga zanga Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sen Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Shawarar Ali Ndume ga Bola Tinubu

Ɗan majalisar ya ce tattaunawa da waɗanda suka shirya zanga-zangar da galibinsu matasa ne zai taimaka wajen yayyafawa abin ruwan sanyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv yau Litinin, Sanata Ndume mai wakiltar Kudancin Borno ya ce:

"Ina tunanin ya kamata shugaban ƙasa ya tattauna da ƴan Najeriya, ya zauna da matasa su yi magana domin daƙile lamarin."

NLC ta aika saƙo ga Shugaba Tinubu

Kalaman Ndume sun yi daidai da matsayar ƙunguyar kwadago NLC, wadda ta shawarci Bola Tinubu ya zauna da masu shirya wannan gagarumar zanga-zanga.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, kungiyar NLC ta ce kamata ya yi Tinubu ya gayyaci jagororin zanga-zangar kuma ya saurari kokensu, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya kafa tarihi, ya ƙirkiro doka kan mata masu iddah a Katsina

Wannan dai na zuwa ne yayin da matasa suka shirya yin zanga-zanga domin nuna fushinsu game da halin ƙunci, yunwa da rashin tsaron da ake fama da su a ƙasar nan.

Hakan ya sa Ali Ndume, wanda majalisar dattawa ta sauke daga matsayin mai tsawatarwa, ya bada shawarin a zauna da matasan domin rarrashinsu.

Hadimin Tinubu ya gano masu shirya zanga-zanga

A wani rahoton kuma hadimin shugaban ƙasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya caccaki magoya bayan Peter Obi kan shirin zanga-zangar da ake yi.

Bayo Onanuga ya bayyana cewa magoya bayan Peter Obi ne ke shirya zanga-zangar da ake yi shirin yi a ranar 1 ga watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262