Peter Obi: 'Yan Adawa Sun Tona Abin da Tinubu Yake Shiryawa Masu Zanga Zanga
- Madugun jam'iyyar Labor, Peter Obi ya caccaki gwamnatin tarayya kan alakanta shi da tayar da tarzoma yayin zanga zanga
- Mai magana da yayun Peter Obi, Yunusa Tanko ne ya yi martani ga gwamnatin tarayya bayan zargin da ta masa na tayar da fitina
- A makon da ya wuce ne gwamantin tarayya ta yi magana kan cewa Peter Obi na cikin masu son harzuka matasa fita zanga zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya yi martani zuwa ga gwamnatin Bola Tinubu.
Peter Obi ya yi martanin ne biyo bayan maganar da mai taimakawa shugaban kasa a harkokin sadarwa, Bayo Onanuga ya yi a kansa kan zanga zanga.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Peter Obi ya yi martanin ne ta hannun mai magana da yawunsa, Yunusa Tanko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bola Tinubu da Peter Obi
A makon da ya wuce ne gwamantin tarayya ta zargi Peter Obi da cewa shi ne mai shirya zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa an yi wa Peter Obi barazanar cewa idan aka samu barna alhakin zai dawo kansa.
Peter Obi ya yi martani ga gwamnati
Mai magana da yawun Peter Obi, Yunusa Tanko ya ce wannan duk barazana ce ta ganin an dakile yan kasa daga hakkin da suke da shi na zanga zanga.
Yunusa Tanko ya kara da cewa kowa ya riga ya san cewa Peter Obi bai taba goyon bayan tarzoma ba kuma ba zai taba goyon bayan tayar da fitina ba.
Tanko: 'Ana son kama Peter Obi'
Haka zalika Yunusa Tanko ya soki maganar da gwamnatin tarayya ta yi a kan batun kama Peter Obi, rahoton Leadership.
Yunusa Tanko ya ce gwamnatin tarayya tana son kama Peter Obi domin ta hana shi fadin albarkacin bakinsa wajen samar da ingantacciyar gwamanti.
Gwamnan Kogi ya gargadi matasa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Najeriya na cigaba da tura gargadi ga matasa kan shirin gudanar da zanga zangar yaki da tsadar rayuwa a fadin ƙasar.
Gwamnatin Kogi ta shiga sahun jihohin da suka isar da sakon gargadi ga matasan Najeriya kan nisantar zanga zangar da ake shirin yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng