Bidiyo: Rarara da Mahaifiyarsa Sun Miƙa Sakon Godiya, Sun Faɗi Sunayen Wasu Manyan Mutane
- Mahaifiyar Rarara ta miƙa godiya ga wasu malamai da sauran al'umma bisa addu'o'in da suka yi na neman Allah ya kuɓutar da ita
- Dauda Kahutu Rarara ya ce mamarsa ce ta matsa sai ta yiwa al'ummar Annabi godiya bayan ta kuɓuta daga hannun masu garkuwa
- Mawakin siyasar ya aika saƙon godiya ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da matarsa, Remi Tinubu da NSA da Malamai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ta miƙa sakon godiya ga wasu Malamai da ƴan Najeriya da suka taimaka mata a lokacin tana tsare a wurin ƴan bindiga.
Hajiya Hauwa’u Adamu ta godewa dukkan al'ummar Annabi waɗanda suka sadaukar da lokacinsu da ƙarfinsu wajen yi mata addu'o'in Allah ya kuɓutar da ita.
Ta yi wannan godiya ne a wani faifan bidiyo da Rarara ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaƴin da take jawabi a kusa da ɗanta Dauda Rarara, Hajiya Hauwa’u ta ce:
"Assalamu Alaikum al'ummar Annabi, na gode Allah ya bada lada Allah ya rufa asiri, da malamai da sauran al'ummar Annabi, na gode Allah ya ba ku lada."
Rarara ya godewa Tinubu da wasu ƙusoshi
Da yake jawabi a bidiyon, Rarara ya bayyana cewa mamarsa ce ta matsa sai ta shiga bidiyon domin ta godewa mutanen da suka taimaka da addu'o'i domin sun yi tasiri.
Bugu da ƙari, fitaccen mawaƙin ya godewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mai ɗakinsa, Sanata Remi Tinubu bisa yadda suka taimaka wajen kuɓutar da Hajiya.
Dauda Kahutu Rarara ya ƙara da miƙa sakon godiya ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa, Nuhu Ribaɗu da Malamai da suka yi addu'o'i.
Mawaƙin ya ambaci sunayen mutane da dama waɗanda ya ce sun taimaka, inda ya ƙara da cewa ba zai yiwu ya faɗi sunan kowa ba saboda mutanen su na da yawa.
DSS ta kama wanda ya sace mamar Rarara
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar DSS a jihar Kano ta tabbatar da cewa ta cafke wani da hannu a sace mahaifiyar Dauda Rarara.
Hukumar ta kai samame ne dajin Makarfi inda ta samu masu garkuwan suna raba kudin fansa da suka karba daga jama'a.
Asali: Legit.ng