Ndume Ya Magantu Kan Barin APC Zuwa PDP Bayan Dakatar da Shi Daga Mukaminsa

Ndume Ya Magantu Kan Barin APC Zuwa PDP Bayan Dakatar da Shi Daga Mukaminsa

  • Kwanaki bayan dakatar da shi daga mukaminsa, Sanata Ali Ndume ya yi martani kan dambarwar da ke faruwa da shi a Majalisa
  • Sanata Ndume ya yi martani kan bukatar ya sauya sheka zuwa PDP ko kuma wata jam'iyya kamar yadda aka sanar da shi
  • Ndume ya ce babu wanda zai iya saka shi ya bar APC saboda yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar tun farkon kafata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Sanata Ali Ndume ya bayyana matsayarsa kan sauya sheka zuwa PDP bayan sukar Bola Tinubu da ya yi wanda ya jawo dakatar da shi.

An dakatar da Ndume ne saboda wasu kalamai da ya yi da ake ganin shugabannin APC da gwamnatin bai musu dadi ba.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya maida martani ga Ganduje, ya faɗi yadda Buhari da Tinubu suka jawo shi APC

Sanata ya yi magana kan komawa PDP daga APC
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya magantu kan makomar siyasarsa. Hoto: @Imrannuhdz.
Asali: UGC

Ndume ya yi magana kan makomar siyasarsa

Sanatan ya bayyana haka ne a Maiduguri da ke jihar Borno a jiya Juma'a 19 ga watan Yulin 2024, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume ya yi martani kan bukatar da aka yi cewa zai iya komawa PDP ko wata jam'iyya da yake bukatar shiga.

Ya ce yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar APC tun farko domin haka magoya bayansa ne za su yanke hukunci kansa, Premium Times ta tattaro.

Ndume ya yi alfahari kan kafa APC

"Ina son in tabbatar muku da cewa ina daga cikin wadanda suka kirkiri jam'iyyar APC tun farko."
"Mutanen mazaba ta da magoya baya ne za su yanke min hukunci kan zama a APC ko shiga wata jam'iyya daban ko kuma barin siyasa."
"Duk abin da suka yanke shawara a kai, ni kuma shi zan bi."

Kara karanta wannan

Kalamai a kan gwamnatin da suka tsumbula Sanata Ndume cikin ruwan zafi a APC da majalisa

- Sanata Ali Ndume

Majalisa ta ki amincewa da hukunta Ndume

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu mambobin Majalisar Dattawa sun ki amincewa da hukunta Sanata Ali Ndume.

Sanata Fasuyi Cyril daga jihar Ekiti shi ya bukaci hukunta Ndume da daukar tsattsauran mataki kansa saboda munanan kalamai ga Majalisar.

Hakan ya biyo bayan dakatar da Ndume daga mukaminsa na shugaban masu tsawatarwa na Majalisar bayan sukar Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.