Tsohon Na Kusa da Peter Obi ya Bayyana Yadda Jagoran na LP Ya Ci Amanar Atiku

Tsohon Na Kusa da Peter Obi ya Bayyana Yadda Jagoran na LP Ya Ci Amanar Atiku

  • A ƙarshe dai tsohon ɗan jam'iyyar adawa Doyin Okupe ya mayar da martani kan zargin da ake masa na cin amanar Peter Obi
  • Wasu dai sun zargi Doyin Okupe da cin amanar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi
  • Okupe ya ce bai ci amanar Peter Obi ba, hasalima shi ne ya ci amanar Atiku Abubakar wanda ya zaɓe shi a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2019

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon darakta janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Doyin Okupe, ya yi watsi da zargin cewa ya ci amanar Peter Obi.

Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, ya zo na uku a bayan Bola Tinubu wanda ya yi nasara da Atiku Abubakar na PDP wanda ya zo na biyu.

Kara karanta wannan

Satar Akuya ta jawo matar aure ta buga wa mijinta gatari, ya mutu nan take

Doyin Okupe ya musanta cin amanar Peter Obi
Doyin Okupe ya ce bai ci amanar Peter Obi ba Hoto: Mr. Peter Obi, Doyin Okupe
Asali: Facebook

A watan Janairu, Okupe ya yi murabus daga jam’iyyar LP, kuma tun daga nan ya kasance yana goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okupe ya musanta cin amanar Peter Obi

Da yake magana a wani faifan bidiyo da aka sanya a shafin X, Okupe, mai shekaru 72, ya mayar da martani ga magoya bayan Peter Obi da suka zarge shi da cin amana.

"Sun ce na ci amanar Peter Obi. Ta yaya zan iya cin amanar Peter Obi? Ta yaya? Babu abin cin amana. Na ɗaya, na shigo siyasa a 1978, ba a san Obi ba a lokacin."
"Domin haka rayuwata da siyasa ta ba dole ba ne sai sun yi daidai da burin Peter Obi. Ba abu ba ne da zai yiwu. Ina yi masa fatan alheri."
"Sannan idan sun ce na ci amanar Bola Tinubu, Atiku Abubakar ne ya jawo Peter Obi domin ya yi masa mataimaki."

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya 'sauya sheka' zuwa APC, ya faɗi abin da ya riƙe shi a PDP

"Amma Peter Obi, saboda burinsa wanda daidai ne, ya bar jam'iyyar PDP sannan ya yi takara da Atiku. Idan kun ce na ci amanar Obi, shi me ya yiwa Atiku? Ba adalci ba ne."
"A siyasa babu maƙiya na dindindin, kowa muradinsa yake karewa. Muradin Peter Obi a 2023 ne ya sanya ya raba gari da tsohon ubangidansa."

- Doyin Okupe

Batun takarar Peter Obi a zaɓen 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban jam’iyyar Labour Party (LP) na ƙasa, Ayo Olorunfemi, ya yi magana kan batun takarar Peter Obi a zaɓen 2027.

Ayo Olorunfemi ya bayyana cewa jam'iyyar ita ce ta fi dacewa Peter Obi ya yi takara a cikinta domin lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng