An Shiga Fargaba Bayan Kazamin Hari Kan Dan Takarar Gwamna a APC, an Rasa Rai

An Shiga Fargaba Bayan Kazamin Hari Kan Dan Takarar Gwamna a APC, an Rasa Rai

  • Wasu miyagu sun kai mummunan hari kan dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo
  • Harin ya yi sanadin mutuwar dan sanda mai tsaron dan takarar na jam'iyyar APC a jiya Alhamis 18 ga watan Yulin 2024
  • Sanata Adams Oshiomole ya yi Allah wadai da harin inda ya ce a yanzu ba lokacin bakar gabar siyasa ba ne da ake yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - An yi ta cece-kuce bayan kai mummunan hari kan dan takarar gwamna a jihar Edo karkashin jam'iyyar APC.

Harin wanda aka kai wa dan takarar APC, Sanata Monday Okpebholo ya yi sanadin mutuwar dan sanda mai tsaronsa guda daya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bindige shugaban Miyetti Allah, kungiyar makiyaya ta yi kira ga mutanenta

An farmaki dan takarar gwamna a jam'iyyar APC
An rasa rai yayin da aka farmaki dan takarar gwamna a APC a jihar Edo. Hoto: Senator Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

An kai hari kan dan takarar APC

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 18 ga watan Yulin 2024 a birnin Benin da ke jihar, Leadership ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin wanda ake zargin jam'iyyar PDP ya jefa shakku a zukatan jama'a yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a watan Satumba.

Daga cikin wadanda suka yi Allah wadai da harin akwai Sanata Adams Oshiomole inda ya nuna goyon baya ga Okpebholo, cewar Vanguard.

Sanata Oshiomole ya dauki zafi kan harin

Sanata Oshiomole ya ce shigar kwamishinan 'yan sanda lamarin ya sake lalata komai inda ya bukaci daukar mataki.

Ya ce wannan hari ya nuna tsandar yadda jam'iyyar PDP takeda kuma irin salon mulkinsu a jihar Edo.

Sanatan ya bukaci babban sifetan 'yan sanda da ya yi gaggawar dauke kwamishinan rundunar a jihar ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan shugabannin APC, ta ci tararsu makudan kudi

An farmaki mataimakin gwamnan Edo

A wani labarin, kun ji cewa an yi ajalin wani dan sanda mai suna Sifeta Onu Ako yayin wata liyafar dawowar mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu.

Lamarin ya faru ne bayan dawowar Shaibu karagar mulki jim kadan bayan hukuncin kotu kan shari'ar da ake yi game da mukaminsa.

Kakakin ‘yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a kan hanyar tashar jirgin sama ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.