Bayan Kotu Ta Dawo da Shi, Mataimakin Gwamnan PDP Ya Kinkimo Sabuwar Rigima
- Mataimakin gwamnan jihar Edo da kotu ta dawo da shi kan mulki ya naɗa sababbin hadimai a ofishinsa ranar Jumu'a
- Kwamared Philip Shaibu ya naɗa shugaban ma'aikata, sakataren watsa labarai da manyan masu taimaka masa na musamman
- Sai dai gwamnatin jihar Edo ta ƙaryata sababbin naɗe-naɗen, inda ta ayyana takardar da ke yawo a matsayin mara tushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo da kotu ta mayar kan mulki, Kwamared Philip Shaibu, ya yi sabbin naɗe-naɗe a ofishinsa.
Waɗanda ya naɗa sun haɗa da Kingsley Ehigiamusor a matsayin shugaban ma'aikatan ofishin mataimakin gwamna da Musa Ebomhiana a sakataren yaɗa labarai.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran mataimakin gwamnan, Ebomhiana ya fitar ranar Jumu'a, jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau Kwamared Shaibu ya sanar da naɗin Emmanuel Akhaba, Charles Olubayo, Mustapha Lawal-Omokpe da Matthias Akhanemhe a matsayin manyan masu taimaka masa na musamman.
Sai kuma Obinson Akhenoba da Robert Ojele waɗanda ya sake naɗa su a matsayin ƙananan masu taimaka masa na musamman.
Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan waɗanda aka naɗa za su kama aiki ne nan take ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya ta soke tsige Shaibu daga matasayin mataimakin gwamna, ta umarci a mayar da shi ofishinsa.
Gwamnatin Edo ya mayar da martani
Sai dai a wani martani da ya mayar, kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama'a na jihar Edo, Chris Nehikhare ya bayyana nade-naɗen a matsayin na ƙarya.
Nehikhare ya ce gwamnati ta lura da wasu takardu da ke yawo a soshiyal midiya cewa an yi naɗe-naɗe a ofishin mataimakin gwamna, Tribune Nigeria ta rahoto.
Kwamishinan ya yi kira ga al'ummar jihar su yi fatali da takardun, inda ya bayyana su a matsayin na ƙarya da ba su da tushe balle makama.
Shaibu ya ce ruhinsa na tare da APC
A wani rahoton kuma kun ji cewa Shaibu ya bayyana kansa a matsayin ɗan APC wanda bai mallaki katin zama cikakken ɗan jam'iyya ba.
Kwamared Philip Shaibu ya bayyana cewa abin da ya riƙe shi a PDP shi ne bai sanar a hukumance ya fice daga jam'iyyar ba.
Asali: Legit.ng