Kwana 1 Bayan Kai Masa Hari, Gwamna Ya Fadi Matsayin Mataimakinsa, Ya Fadi Dalili

Kwana 1 Bayan Kai Masa Hari, Gwamna Ya Fadi Matsayin Mataimakinsa, Ya Fadi Dalili

  • Kwanaki biyu bayan hukuncin kotu game da mukamin Philip Shaibu, gwamnatin jihar ta fadi matsayinsa duk da hukuncin
  • Gwamnatin jihar ta ce har yanzu Philip Shaibu korarren mataimakin gwamna ne kuma ta daukaka kara kan lamarin
  • Wannan na zuwa ne bayan Babbar Kotun jihar ta dawo da Shaibu mukaminsa bayan tsige shi da aka yi kwanakin baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamnatin jihar Edo ta yi martani bayan hukuncin kotu da ya dawo da mataimakin gwamna, Philip Shaibu.

Gwamnatin jihar ta ce duk da hukuncin kotun, har yanzu Shaibu korarren ne daga mukaminsa na mataimakin gwamnan jihar.

Gwamna ya bayyana matsayin mataimakinsa da aka kora
Gwamnatin jihar Edo ta ce har yanzu Philip Shaibu korarre ne. Hoto: Godwin Obaseki, Philip Shaibu.
Asali: Twitter

Gwamnati ta yi wa mataimakin gwamna martani

Kara karanta wannan

"Ban ce zan biya N80,000 ba," Gwamna ya musanta rahoton zai yi karin albashi

Kwamishinan yada labarai a jihar, Chris Osa shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 19 ga watan Yulin 2024, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osa ya ce babu wanda zai dawo da Shaibu har sai idan Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan rigimar da ake yi a jihar, Punch ta tattaro.

Wannan martanin na gwamnatin na zuwa bayan dawo da Shaibu da Babbar Kotun jihar ta yi game da korafin da ya shigar.

Gwamnatin ta ce ta daukaka kara zuwa kotun gaba inda ta ce za ta bi dukkan matakai da tsare-tsare na shari'a kan lamarin.

Gwamnatin Edo ta daukaka kara kan Shaibu

"Har yanzu Philip Shaibu korarren mataimakin gwamna ne a jihar Edo har sai idan Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci."
"Bayan hukuncin Babbar Kotun jihar a ranar Laraba 17 ga watan Yulin 2024, gwamnatin Edo ta daukaka kara kan lamarin."

Kara karanta wannan

Uba Sani ya ba da umarnin a zane Dan Bilki Kwamanda? Gwamnatin Kaduna ta magantu

"Shaibu ya take doka inda ya tattaro 'yan ta'adda da muggan makamai a filin jirgin sama bayan hukuncin kotu domin tayar da tarzoma."

- Chris Osa

Philip Shaibu ya tsallake rijiya ta baya

Kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya tsallake rijiya ta baya bayan wani hari da aka kai masa a jihar.

Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan kotu ta dawo da shi kan mukaminsa na mataimakin gwamnan jihar bayan an tsige shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.