Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shugabannin APC, Ta Ci Tararsu Makudan Kudi

Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shugabannin APC, Ta Ci Tararsu Makudan Kudi

  • Babbar kotun jihar Rivers ta tanadi hukunci kan shari'ar da ake yi bayan korar shugabannin jam'iyyar APC
  • Kotun ta dauki matakin ne a yau Juma'a 19 ga watan Yulin 2024 inda alkalin kotun ya umarci biyan tara N300,000
  • Wannan na zuwa ne bayan matakin da aka dauka na korar shugabannin jam'iyyar a jihar da kananan hukumomi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Babbar kotun jihar Rivers ta yi zama kan takaddama game da dambarwar shugabancin jam'iyyar APC.

Kotun da ke zamanta a birnin Port Harcourt ta tanadi hukunci kan shari'ar bayan korar shugabannin jam'iyyar APC.

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar korar shugabannin jam'iyyar APC
Babbar kotun jihar Rivers ta tanadi hukunci kan shari'ar shugabancin jam'iyyar APC. Hoto: @OfficialAPCNg.
Asali: Twitter

Kotu ta yi hukunci kan shugabannin APC

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: NLC ta yi barazanar tsunduma wani yajin aiki, an gano dalili

Alkalin kotun, Mai Shari'a Sika Aprioku shi ya dauki matakin a yau Juma'a 19 ga watan Yulin 2024 a jihar, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aprioku bayan sauraran korafe-korafe daga bangarorin biyu ya ce zai tuntube su a cikin awanni 48 domin sanin matakin gaba.

Wannan na zuwa ne bayan korar shugabannin APC na jihar da kananan hukumomi karkashin jagorancin Emeka Beke, cewar Independent.

Rivers: Wadanda ake kara kan shugabancin APC

Kwamitin jam'iyyar mai mutane bakwai karkashin jagorancin Cif Tony Okocha su ake kara a kotun domin neman yi musu adalci.

Wadanda ake kara a shari'ar sun hada da Sam Sam Etetegwung da duka shugabannin APC da sufetan 'yan sanda da kuma hukumar zabe ta INEC.

Bayan daukar matakin, ya umarci biyan tara har N300,000 ga wadanda suke korafi kan shugabannin jam'iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

Kotu ta raba gardama kan takaddamar neman tuge gwamnan PDP, ta jero dalilai

Kotu ta yi hukunci a zaben gwamna

Kun ji cewa Kotun Daukaka Kara ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka yi a watan Nuwambar 2023.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwaman da aka gudanar.

Hakan ya biyo bayan samun nasara a zaben bayan hukumar zabe ta INEC ta sanar da shi wanda ya yi nasara a watan Nuwambar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.