APC Ta Yi Martani Mai Zafi Bayan PDP Ta Fara Harin Kwace Mulki a 2027

APC Ta Yi Martani Mai Zafi Bayan PDP Ta Fara Harin Kwace Mulki a 2027

  • Jam'iyyar APC ta yi zazzafan martani ga PDP biyo bayan maganganu da gwamnonin jam'iyyar suka yi bayan kammala wani taro
  • A jiya Alhamis, jami'in yada labaran APC, Barista Felix Morka ya yi martanin inda ya ce PDP ba ta da wani hurumin zarginsu a Najeriya
  • Felix Morka ya kuma bayyana irin kokarin da shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi wajen ganin lamura sun daidaita a fadin Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Cacar baki ta barke tsakanin jami'yyar PDP da APC a kan shirin zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Hakan na zuwa ne bayan PDP ta yi taro a Enugu ta fadi hanya da za a bi wajen kawo sauki a Najeriya da ta zargi APC da saka al'umma.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya 'sauya sheka' zuwa APC, ya faɗi abin da ya riƙe shi a PDP

Jam'iyyar APC
APC ta yi martani ga PDP kan wahalar rayuwa a Najeriya. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Biyo bayan haka ne APC ta yi martani a kan kalaman PDP kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan da PDP ta yi kan mulkin APC

Legit ta ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta ce hanya daya ce ta magance matsalolin Najeriya, ita ce kayar da APC a zaben 2027.

Saboda haka ne ma PDP ta ce idan ta dawo mulki komai zai dawo daidai kamar lokacin da ta yi mulki a baya,.

APC ta yi martani ga shugabannin PDP

Jami'in yada labaran APC na kasa, Barista Felix Morka ya ce maganar da PDP ba gaskiya ba ne kuma mulkinsu na shekaru 16 ne ya jefa Najeriya a wahala.

Felix Morka ya kara da cewa halin kunci da ake ciki a yanzu na kankanin lokaci ne domin Bola Tinubu ya dauki hanyar gyara Najeriya.

Kara karanta wannan

"Sun yi barazanar kashe ni," Dan Bilki ya nace gwamna Uba Sani ne ya sa a zane shi

APC ta ce 'Gwamnonin PDP sun rikice'

Felix Morka ya ce abin mamaki ne yadda gwamnonin PDP suke murna kan yancin kananan hukumomi da Bola Tinubu ta samar amma kuma suna wani kuka na daban.

Ya ce hakan alama ce ta cewa sun rikice tun da an kawo abin da suka gaza samarwa amma kuma suna wani korafi, rahoton Leadership.

APC ta saka labule kan jihohin kudu

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta ci gaba da shirye-shiryen yadda za ta karɓe mulkin wasu jihohi

Ganduje, Sanata Ifeanyi Ubah da wasu manyan kusoshin APC daga jihar Anambra sun gana a wani Otal da ke birnin tarayya Abuja a kan batun siyasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng