Mataimakin Gwamna Ya 'Sauya Sheka' Zuwa APC, Ya Faɗi Abin da Ya Riƙe Shi a PDP

Mataimakin Gwamna Ya 'Sauya Sheka' Zuwa APC, Ya Faɗi Abin da Ya Riƙe Shi a PDP

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo wanda aka mayar kan muƙaminsa ya ce gangar jikinsa kaɗai ta rage a PDP amma tuni ya koma APC
  • Kwamared Philip Shaibu ya bayyana cewa abin da ya riƙe shi a PDP shi ne bai sanar a hukumance ya fice daga jam'iyyar ba
  • Game da batun goyon bayan ɗan takarar gwamna na APC, Shaibu ya ce yana da ikon marawa duk wanda ya ga dama baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo da aka mayar kan muƙaminsa, Kwamared Philip Shaibu ya nuna alamun ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Kwamared Phillip Shaibu ya ce abu ɗaya da rage masa gabanin ya zama cikakken 'dan APC, shi ne sanarwa a hukumance ya bar PDP zuwa jam'iyya mai-ci.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya zama na farko a Arewa da ya amince zai fara biyan ma'aikata N70,000

Kwamared Philip Shaibu.
Mataimakin gwamnan Edo ya yi ikirarin cewa shi ɗan APC mara rijista a hukumance Hoto: Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

Menene ya rike Philip Shaibu a PDP?

'Dan siyasar ya ce abin da ke ci gaba da rike shi a jam’iyyar PDP shi ne har yanzu bai miƙawa jam’iyya mai mulki a Edo takardar ficewarsa a hukumance ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Philip Shaibu ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa yake goyon bayan dan takarar gwamnan APC a Edo a cikin shirin Arise TV yau Juma’a. 

Idan za ku iya tunawa babbar kotun tarayya karkashin mai shari'a J. K. Omotosho ta soke mataki majalisar dokokin Edo na tsige Shaibu daga kujerar mataimakin gwamna.

Shaibu ya jaddada goyon bayan APC

A rahoton Daily Trust, Shaibu ya bayyana cewa har yanzu bai fice daga jam’iyyar PDP a hukumance ba, amma ya riga ya haɗe da APC.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: Sanata Ndume ya mayar da martani kan sauke shi a muƙamin Majalisa

"A PDP yanzu kowa na iya goyon bayan wanda ya ga dama. Dangane da batun goyon bayan dan takara kuma tsarin mulki ya bamu ƴancin goyon bayan wanda kake so a kowace jam’iyya.
"Abin da ya tsayar da ni a PDP shi ne ban sanar a hukumance ba, amma a zahirin gakiya ni ɗan APC ne wanda bai yi rijista a hukumance ba. Gangar jikina kaɗai ta rage a PDP."

- Kwamared Philip Shaibu.

Gwamnan Edo ya tsige kwamishina

A wani rahoton kuma Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya sallami kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Samuel Alli daga kan muƙaminsa ba tare da wani ɓata lokaci ba

Sakataren gwamnatin jihar, Osarodin Ogie ya tabbatar da korar kwamishinan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262