"Sun Yi Barazanar Kashe Ni," Dan Bilki ya Nace Gwamna Uba Sani ne Ya Sa a Zane shi

"Sun Yi Barazanar Kashe Ni," Dan Bilki ya Nace Gwamna Uba Sani ne Ya Sa a Zane shi

  • Bayan tsumagiya da aka rika shauda masa bisa zargin zagin gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, jigon APC Dan Bilki Kwamanda ya magantu
  • An gano Dan Bilki ta cikin wani faifan bidiyo tare da nuna shatin dukan da wasu da ya kira da jami'an tsaro su ka yi masa a Kaduna
  • AbdulMajeed dan bilki ya zargi gwamna Uba Sani da bayar da umarnin a lakada masa duka, duk da gwamnatin Kaduna ta musanta haka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - A yayin da kafafen sada zumunta su ka dauki dumi a kan bulalar da jigon APC a Kano, AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda ya sha, masoyin Buharin ya yi jawabi.

Kara karanta wannan

Kano: Sarki Sanusi II ya koka kan halin kunci da ake ciki, ya yabawa gwamnatin Abba

A safiyar ranar Alhamis aka gano wani faifan bidiyo inda wasu da aka yi zargin jami'an tsaro ne su ka yi ta tsula wa Dan Bilki bulala.

Uba da Kwamanda
Dan Bilki Kwamanda ya zargi Gwamnan Kaduna da bayar da umarnin lakada masa duka Hoto: AbdulMajeed Almustapha Kwamanda/Senator Uba Sani
Asali: Facebook

A bidiyon da wani mai amfani da manhajar Facebook, Isah Magaji Rijiya Biyu ya wallafa, an gano jikin AbdulMajeed Kwamanda burdin burdin da shatin bulala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan sanda sun yi mani barazana," Dan Bilki

Jigo a jam'iyyar APC, AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda ya bayyana yadda aka yi wasu da ake zargin jami'an tsaro ne su ka kamashi.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Mafitar Arewa a Youtube, an gano Dan Bilki zaune a gefen gadon asibiti, jikinsa duk shatin duka.

Dan Bilki Kwamanda ya ce jami'an sun yi barazanar kashe shi, inda su ka kai shi bakin ruwa tare da barazanar jefa shi a ciki ya mutu.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya ba da umarnin a zane Dan Bilki Kwamanda? Gwamnatin Kaduna ta magantu

Abin da Dan Bilki ya fadawa duniya

"Wannan duk abin da ku ke gani dukansu ne. Bakin ruwa ma su ka kai ni, su ka ce za su kashe ni, su jefa ni a ruwa a banza."
"Ka ga ke nan Uba Sani ne ya sa aka yi min wannan wulakancin duka da bulala."

- AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda

Tuni gwamnatin Kaduna ta fitar da sanarwa ta na nesanta kanta da dukan da aka yiwa Dan Bilki, tare da umartar a gudanar da bincike a kan lamarin.

An zane Dan Bilki Kwamanda a Kaduna

A baya mun kawo labarin cewa jigo a jam'iyyar APC reshen jihar Kano, AbdulMajeed Dan rBilki Kwamanda ya sha bulala bayan da aka yi zargin ya je har Kaduna ya na zagin gwamna.

Wadanda aka gani cikin bidiyon da dan Bilki ya shaida a matsayin jami'an tsaro sun dage su na dukansa, inda su ka tambayi dalilinsa na zagin gwamna Uba Sani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.