Zaben 2027: An Fadawa Tinubu Sirri 3 Domin Shawo Kan Talakan Najeriya Cikin Sauki

Zaben 2027: An Fadawa Tinubu Sirri 3 Domin Shawo Kan Talakan Najeriya Cikin Sauki

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya tura sako ga Bola Tinubu kan tafiyar da mulkin Najeriya
  • Dele Momodu ya ce ya fahimci cewa duk ƙoƙarin da Bola Tinubu yake na raba tallafi na cikin neman samun mulki karo na biyu
  • Saboda haka ya bayyanawa shugaba Bola Tinubu hanyoyin da ya kamata ya bi wajen samun nasara a zaben shekarar 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Dele Momodu ya bayyanawa Bola Tinubu hanyar da zai shawo kan talakawan Najeriya.

Dele Momodu ya fadi haka ne a cewarsa saboda ya kalli take taken Bola Tinubu na neman zabe karo na biyu.

Kara karanta wannan

Tsige Ndume: Tinubu ya kara rasa goyon bayan manyan yan siyasa

Shugaba Tinubu
An ba Tinubu shawara kan zaben 2027. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Dele Momodu ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyoyin da Tinubu zai shawo kan talakawa

1. Samar da sana'o'i hannu ga matasa

Dele Momodu ya bayyana cewa idan Bola Tinubu na son shawo kan al'umma to dole ya mayar da hankali kan koyon sana'a ga matasa.

Ya ce akwai buƙatar a tallafi matasa masu hazaka da aiki tukuru wajen samun abin yi a Najeriya.. domin hakan zai taimaka masa a zaben 2027

2. Gyara harkokin ilimi a Najeriya

Haka zalika Dele Momodu ya ce akwai bukatar bunkasa harkokin ilmi a Najeriya idan ana son samun hadin kan al'umma.

Saboda haka ne ma ya bukaci Bola Tinubu da ya inganta makarantun Najeriya domin samar da ilimi ingantacce.

3. Haɓaka harkokin noma a Najeriya

Kara karanta wannan

"Tinubu na kokari, kar ku shiga zanga zanga," Minista ya lallabi jama'a

Abu na uku da Dele Momodu ya ambata da zai ba Bola Tinubu nasara a 2027 shi ne habaka harkokin noma a Najeriya.

Dele Momodu ya bayyana cewa dole a kashe kudi da kayan aiki yadda ya kamata wajen habaka noma da manoma idan ana son samun nasara.

A ƙarshe, Dele Momodu ya ce dukkanin rabon kudi da kayan tallafi da Tinubu yake yi ba za su amfane shi da komai ba a 2027.

Tinubu ya nada sabon mukami

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Didi Esther Walson-Jack a matsayin sabuwar shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Esther Walson-Jack za ta maye gurbin shugabar ma'aikatan, Dr Folasade Yemi-Esan wanda za ta yi ritaya daga aiki a ranar 13 ga watan Agusta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng