"Abin Takaici, Majlisa ta Zama 'Yar Amshin Shata," Atiku ya Caccaki Sauke Sanata Ali Ndume

"Abin Takaici, Majlisa ta Zama 'Yar Amshin Shata," Atiku ya Caccaki Sauke Sanata Ali Ndume

  • Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki yadda ya ce majalisa ta zama ‘yar amshin shatan fadar shugaban kasa
  • Atiku ya na kakkausar suka ne bayan majalisa ta tsige bulaliyarta Sanata Ali Ndume bisa sukar gwamnatin tarayya
  • Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne ya ce aikin majalisa shi ne tabbatar da fadar shugaban kasa ta yi aikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki majalisa kan yadda ta tsige bulaliyarta, Sanata Ali Ndume saboda sukar shugaban kasa.

Majalisa ta tsige Sanata Ndume daga mukaminsa bayan jam'iyyar APC ta rubuta zungureriyar wasika ta na kalubalantar kalaman Sanatan kan shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An fadawa Tinubu sirri 3 domin shawo kan talakan Najeriya cikin sauki

Atiku
An zargi majalisa da zama 'yar amshin shata Horo: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa a wata hira da Sanata Ndume ya yi da manema labarai, ya ce Tinubu ba shi da masaniya a kan abin da ke faruwa a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yan majalisa su yi aikinsu” Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce lokaci ya yi da ‘yan majalisa za su takawa dabi'unsu birki.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin yadda ‘yan majalisa su ka zama marasa ra'ayin kansu.

Ya ce idan aka ci gaba da irin wannan alaka tsakanin majalisa da gwamnatin tarayya, baki daya dimokuradiyyar ta dauko lalace wa.

Menene ayyukan 'yan majalisa?

Atiku Abubakar ya ce ayyukan da majalisa ya kamata ta yi shi ne tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba ta wuce gona da iri ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya buƙaci Sanata ya fice daga APC mai mulki ya koma jam'iyyar adawa

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce aikin majalisa ne kare jama’a daga karan tsayen da gwamnatin tarayya ka iya yi ga al'ummarta

Majalisa ta ba Sanata Ndume mukami

A baya mun ruwaito cewa majalisar kasar nan ta gaggauta yiwa Sanata Ali Ndume mukami awanni bayan ta tsige shi daga mukaminsa na bulaliyar majalisa.

Ndume ya jawo fushin jam'iyyar APC har ta kai ga tsige shi bayan kalaman sukar yadda gwamnatin Tinubu ke gudanar da mulkin 'yan Najeriya da ke cikin halin matsi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.