Sadaukar da Rabin Albashi: ’Yan Najeriya Sun Aika Sako Ga ’Yan Majalisar Wakilai
- 'Yan Najeriya sun caccaki 'yan majalisar wakilan Najeriya bayan sun zabtare kaso 50% na albashinsu domin rage radadin talakawa
- Tuni jama'a suka ce ai ba su san asalin albashin nasu ba, kuma alawus dinsu ya fi dacewa su zabtare ba albashin ba
- Wasu sun zargi cewa, jin za a fita gangamin zanga-zanga ne ya kawo hakan, za a fi samun sakamakon idan an fita baki ɗaya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
'Yan Najeriya sun yi martani ga 'yan majalisar wakilan Najeriya bayan sun sanar da zabtare rabin albashinsu a matsayin gudumawarsu na saukaka matsin rayuwa ake ciki a kasar nan.
Legit Hausa ta ruwaito cewa mataimakin kakalin majalisar wakilai, Benjami Okezie Kalu ne ya mika roko ga 'yan majalisar na su sadaukar da kashi 50 na albashinsu na watanni shida.
Manufar 'yan majalisa na zabtare albashi
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan Najeriya sun yi martani kan wannan mataki da 'yan majalisar suka dauka wanda zai iya samar da N180m a cikin watanni shida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin kakakin majalisar ya ce za a yi amfani da albashin da aka zabtare wurin tallafawa kokarin gwamnatin tarayya na shawo kan hauhawar farashin kayan abinci a kasar nan.
Ta hanyar zabtare albashin da kashi hamsin cikin dari, 'yan majalisar wakilan 360 za su sadaukar da N108m na watanni shida masu zuwa.
'Yan Najeriya sun aika sako ga 'yan majalisa
Sai dai kuma, 'yan Najeriya masu tarin yawa sun je sahar sada zumunta tare da caccakar wannan yunkurin, inda wasu suka bukaci 'yan majalisar da su zabtare alawus dinsu maimakon albashi.
A dandalin sada zumunta na X, wanda aka sani da Twitter a baya, ga kadan daga cikin martanin da 'yan Najeriya suka yi:
@donchia ya ce:
“Wannan fa ya faru ne sakamakon sanar da shirin yin zanga-zanga, ku yi tunanin abinda za mu iya cimmawa idan muka hada kai muka ce mun gaji da abin da ke faruwa."
@Comr_lucky1 ya rubuta cewa:
“Ba wai batun zabtare albashinku ba ne, ya kamata ku ma a rika biyanku da mafi ƙarancin albashi, wannan ne abinda yafi dacewa, akasin hakan kuwa duk laifi ne."
@AbekheMA ya ce:
“Amma mun ma san asalin albashinsu? To ya za mu tabbatar da zabtare kashi 50 cikin 100? An lullube albashin 'yan majalisa cikin sirri, ta yadda ba za mu san abinda suke samu ba."
@maniac8989 ya ce:
"Ku zabtare alawus dinku ba wai albashi ba. Mun san albashin ku bai wuce cikin cokali ba idan aka kwatanta da alawus-alawus dinku."
Tinubu ya fadi sabon mafi karancin albashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya gana da kungiyoyin kwadago a yau Alhamis, inda suka cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi.
Shugaban kasar ya ayyana N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya kuma za a rika waiwayar dokar albashin duk bayan shekaru uku.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng