Da duminsa: Yan majalisar wakilai 360 zasu bada albashinsu na watanni biyu don yakar COVID-19
Dukkan mambobin majalisar wakilan tarayya sun yarje da bada gudunmuwar albashinsu na watanni biyu domin kawo karshen annobar cutar Coronavirus a Najeriya.
Kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana hakan ne a faifan bidiyon da ya saki a shafinsa na Soshiyal Midiya ranar Talata, 31 ga Maris, 2020.
Gbajabiamila ya bayyana cewa wannan shine gudunmuwar da yan majalisar zasu bada domin rage radadi kan al'ummar mazabarsu a wannan lokaci mai wuya da ake ciki.
Yace: "A matsayinmu na yan majalisar wakilar tarayya, mun yi alkawarin bada dukkan albashinmu na watanni biyu masu zuwa domin yakar cutar COVID19 a Najeriya."
"Wannan kudi zai zama taimako ga ma'aikatan kiwon lafiya dake aiki tukuru, sannan sauran yan Najeriya domin jin dadinsu cikin wannan lokaci mai wuya."
"Saboda haka, na umurci magatakardan majalisar dokokin tarayya ya tabbatar da cewa an tura albashin dukkan mambobin majalisa asusun tallafin."
KU KARANTA Coronavirus: Mutane biyu da suka kamu a Kaduna na kusa da El-Rufa'i ne - Gwamnatin jihar
A bangare guda, Mambobin majalisar dattawan Najeriya sun yanke shawarar ba da gudunmuwar rabin albashinsu fari daga watan Maris domin yakar cutar Coronavirus da ta addabi Najeriya.
Mukaddashin kakakin majalisar, Godiya Akwashiki, ya sanar da hakan ne ranar Litinin a wnai jawabi.
Jawabin yace: "Bayan shawara kan yadda ake bada gudunmuwa wajen ganin karshen annobar Coronavirus a Najeriya, majalisar dattawa na sanar da cewa fari daga watan Maris, sanatoci za su rika bada gudunmuwar rabin albashinsu na wata domin yakar wannan cutar."
"Yan majalisar dattawa za su cigaba da bada rabin albashinsu na wata har sai an an ga bayan cutar Coronavirus a Najeriya."
"Majalisar dattawar ta jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa kan namijin kokarin kare kasa daga annobar."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng