Kotu Ta Raba Gardama Kan Takaddamar Neman Tuge Gwamnan PDP, Ta Jero Dalilai
- Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Douye Diri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa
- Kotun bayan tabbatar da nasarar Diri ta kuma yi fatali da korafin jam'iyyar APC da dan takararta, Timipre Sylva a jihar
- Hakan ya biyo bayan tabbatar da Gwamna Diri da hukumar INEC ta yi a matsayin wanda ya lashe zaben watan Nuwambar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa - Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan zaben gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri da mataimakinsa, Lawrence Oborwahariewo.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Diri na jam'iyyar PDP inda ta yi fatali da korafin jam'iyyar APC da ke kalubalantar zaben.
Bayelsa: Hukuncin kotu kan zaben gwamna
Alkalan kotun guda uku sun yanke hukuncin ne a yau Alhamis 18 ga watan Yulin 2024, TheCable ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta fatattaki korafin dan takarar jam'iyyar APC, Timipre Sylva a zaben da aka gudanar a watan Nuwambar 2023, cewar Channels TV.
Ta ce kotun sauraran kararrakin zabe a jihar ta yi hukuncin gaskiya da ta yi fatali da korafin Sylva da kuma jam'iyyarsa ta APC.
Kotu ta yi fatali da korafin APC
Har ila yai, kotun ta umarci Sylva da jam'iyyar APC su biya diyyar N500,000 ga wadanda ake kalubalanta a shari'ar.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar INEC ta tabbatar da Douye Diri da mataimakinsa, Lawrence Oborwahariewo a matsayin wadanda suka lashe zaben.
Daga bisani, Sylva da jam'iyyar APC sun ki amincewa da hukuncin kotun inda suka daukaka kara domin neman hakkinsu.
Kotu ta yi hukunci kan zaben gwamnan Imo
A wani labarin, kun ji cewa Kotun Daukaka Kara ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Imo da aka gudanar a karshen 2023.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Hope Uzodinma na jam'iyyar APC tare da fatali da korafin jam'iyyar PDP a jihar.
Hakan ya biyo bayan samun nasara a kotun kararrakin zabe da Gwamna Uzodinma ya yi bayan lashe zabe a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng