'Yancin Kananan Hukumomi Zai Tabbata, Majalisa Za Ta Ƙirƙiri Hukumar Zabe Ta Musamman
- Kwanaki kadan bayan samun ƴancin kananan hukumomi, Majalisar Tarayya na kokarin kirkirar hukumar zabe ta musamman
- Sanata Sani Musa da ke wakiltar Niger ta Gabas shi ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar a yau Alhamis 18 ga watan Yulin 2024
- Hakan ya biyo bayan hukuncin Kotun Koli a makon jiya game da ƴancin ƙananan hukumomi a fadin ƙasar baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Majalisar Dattawa a Najeriya ta dauki mataki domin tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomi.
Mambobin Majalisar sun shirya ƙirƙirar hukumar zabe da za ta rika gudanar da zabukan kananan hukumomi.
Za a kirkiri hukumar zaben kananan hukumomi
Sanatan da ke wakiltar Niger ta Gabas, Sani Musa shi ya gabatar da kudirin a gaban Majalisar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuni kudirin ya tsallake karatu na farƙo a dakin Majalisar wanda ake sa ran zai taimakawa wurin dakile ikon gwamnoni kan ƙananan hukumomi.
Idan kudirin ya tabbata, hukumar za ta kasance daya tilo da za ta rika gudanar da zabukan kananan hukumomi a fadin kasar, The Nation ta tattaro.
Matakin kotu kan ƴancin kananan hukumomi
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan hukuncin Kotun Koli game da ƴancin ƙananan hukumomi a Najeriya.
Kotun ta umarci Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ƙananan hukumomi kudinsu daga asusunta kamar yadda take yi wa gwamnoni.
Ta gargadi gwamnonin jihohi kan ci gaba da nuna iko musamman kan kudin ƙananan hukumomi da ke shigowa.
Wasu daga cikin tsofaffin gwamnoni da dama sun soki matakin kotun kan lamarin kananan hukumomi inda suka ce hakan koma baya ne ga kasar baki daya.
Halin kunci: Majalisa ta rage albashin mambobinta
Mun kawo labarin cewa Majalisar Wakilai a Najeriya ta zaftare albashin mambobinta domin tallafawa al'umma yayin da ake shan fama.
'Yan Majalisar sun amince da rage 50% na albashinsu saboda tallafawa al'umma yayin da ake cikin halin ƙunci a kasar.
Mataimakin kakakin Majalisar, Benjamin Kalu shi ya gabatar da bukatar a gaban Majalisar a yau Alhamis 18 ga watan Yulin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng