Majalisa Na Shirin Kawo Tsarin da Zai Ba Tinubu Damar Zarce Shekara 4 Ba Tare da Zabe Ba

Majalisa Na Shirin Kawo Tsarin da Zai Ba Tinubu Damar Zarce Shekara 4 Ba Tare da Zabe Ba

  • A jiya Laraba majalisar wakilan tarayya ta yi karatu na daya ga kudurin da zai canza fasalin kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Kudurin na nufin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki na shekarar 1999 wanda zai shafi mulkin shugaban kasa da gwamnoni
  • Idan kudurin ya tabbata, shugaban kasa, gwamnonin jihohi da ciyamomi za su huta da wahalar neman zabe karo na biyu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta fara tattaunawa kan neman canza fasalin kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

A jiya Laraba, 17 ga watan Yuli majalisar wakilai ta yi karatu na daya ga kudurin canza kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kansiloli sun taru sun tsige shugaban karamar hukuma, ana zarginsa da ta'asar kudi

Majalisar wakilai
Majalisa ta fara kokarin kawo gyara a kundin mulkin Najeriya. Hoto: Abbas Tajudden
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa idan aka zartar da kudurin za a kara tsawon shekarun shugabanni a kan mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan majalisa da suka kawo kudurin

Rahotanni sun tabbatar da cewa dan majalisa daga jihar Imo, Ikenga Ugochinyere ne ya fara kawo kuɗurin.

Bayan gabatar da kudurin, Ikenga Ugochinyere ya samu goyon bayan yan majalisun tarayya kimanin 50, rahoton Sahara Reporters.

Wandada za su ci moriyar tsarin

Bincike ya nuna cewa idan aka rattaba hannu a kan tsarin, shugaban kasa da mataimakinsa na cikin wadanda za su ci moriyar tsarin.

Haka zalika dukkan gwamnonin jihohi su 36 da shugabannin kananan hukumomi za su ci moriyar tsarin.

Shekara nawa za a dawo yi kan mulki?

Ana sa ran cewa idan aka samu amincewa da tsarin shugaban kasa, gwamnoni da ciyamomi za su rika yin shekaru shida a kan mulki.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Hakan na nuni da cewa shugabannin za su rika yin mulki sau daya ne kawai ba tare da yin tazarce ba.

Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilai ta gayyaci jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan umurnin noma da shugaba Bola Tinubu ya ba sojoji.

Ana sa ran cewa shugabannin tsaro za su yi gamsasshen bayani ga majalisar wakilai kan yadda za su cika umurnin shugaban kasa Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng