Ganduje Ya Sa Labule da Minista da Manyan Kusoshin APC a Abuja, An Gano Dalilin Zaman

Ganduje Ya Sa Labule da Minista da Manyan Kusoshin APC a Abuja, An Gano Dalilin Zaman

  • Jam'iyyar APC karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta ci gaba da shirye-shiryen yadda za ta karɓe mulkin wasu jihohi a Kudu maso Gabas
  • Ganduje, Sanata Ifeanyi Ubah da wasu manyan kusoshin APC daga jihar Anambra sun gana a wani Otal da ke birnin tarayya Abuja a ranar Laraba
  • Wata majiya daga hedkwatar APC ta bayyana cewa taron ya tattauna kan wanda jam'iyyar za ta tsayar takara a zaɓen gwamnan Anambara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Anambra Sanata Ifeanyi Ubah ya yi ganawar sirri da shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a Abuja.

Abdullahi Ganduje ya yi wannan ganawa da Sanata Ubah tare da wasu manyan ƙusoshin jam'iyyar APC daga jihar Anambra da ke shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 6 game da Sanatan da ya karɓi matsayin Ndume a Majalisa

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Shugaban APC ya sa labule da Sanata Ubah da. wasu manyan kusoshin APC a Abuja Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Minista, ƙusoshin da suka halarci zaman APC

Taron wanda ya gudana a Otal din Nicon Luxury a birnin tarayya ya samu halartar ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohaneye, kamar yadda Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran jiga-jigan APC daga Anambra da suka halarci zaman sun haɗa da shugaban APC na jiha, Chief Basil Ejidike da mataimakin sakataren tsare-tsare na kasa, Nze Chidi Duru.

Wannan zama na zuwa ne kwanaki biyu bayan jam'iyya mai mulki ta sanar da shirinta na yin aiki tuƙuru domin karbe mulkin jihohin Abia da Enugu a zaɓen 2027.

Sai dai har kawo yanzu babu wasu cikakkun bayanai kan batutuwan da aka tattatuna a wannan taro da ya gudana ranar Laraba da daddare.

APC na shirin tsayar da Sanata Ubah

Amma wata majiya ta shaidawa ƴan jarida cewa an kira taron gaggawar ne domin tsayar da Sanata Ubah a matsayin ɗan takarar gwamna a inuwar APC a zaɓen Anamba da ke tafe.

Kara karanta wannan

Ganduje ya buƙaci Sanata ya fice daga APC mai mulki ya koma jam'iyyar adawa

"Na fahimci jam'iyya mai mulki na neman fitaccen dan siyasa da zai iya karɓe mulki daga hannun gwamnatin APGA a Anambra kuma watakila ta amince da Sanata Ifeanyi Ubah."

Ubah, wanda aka sake zabensa a matsayin sanata a karkashin inuwar jam’iyyar YPP a zaɓen da ya wuce, ya koma APC ne a watan Oktoban 2023, Politics Nigeria ta ruwaito.

APC ta bukaci Ndume ya koma adawa

A wani labarin kun ji cewa jam'iyyar APC ta shawarci sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Muhammed Ali Ndume ya sauya sheka zuwa wata jam'iyyar adawa.

Hakan ya biyo bayan sauke Ndume daga matsayin mai tsawatarwa a majalisar dattawa sakamakon sukar da ya yi wa Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262