Bayan Tsige Ndume, 'Yan Majalisa Sun Kaure Kan Hukunta Sanatan, Sun Fadi Matsaya

Bayan Tsige Ndume, 'Yan Majalisa Sun Kaure Kan Hukunta Sanatan, Sun Fadi Matsaya

  • Mambobin Majalisar Dattawa a Najeriya sun yi fatali da kokarin daukar tsattsauran mataki kan Sanata Ali Ndume
  • Sanatan da ke wakiltar Ekiti ta Arewa, Fasuyi Cyril shi ya bukaci haka a zaman Majalisar a yau Laraba 17 ga watan Yulin 2024
  • Wannan na zuwa ne bayan matakin da Majalisar ta ɗauka kan Ndume na dakatar da shi a matsayin mai tsawatarwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mambobin Majalisar Dattawa a Najeriya sun ki amincewa da bukatar daukar mataki kan Sanata Ali Ndume.

Mambobin sun yi fatali da hakan ne bayan Sanata Fasuyi Cyril da ke wakiltar Ekiti ta Arewa ya bukaci a hukunta Ndume.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba JAMB sabon umarni kan adadin shekarun shiga jami'o'i da makarantu

Mambobin Majalisa sun yi bore kan bukatar hukunta Ndume
Mambobin Majalisar Dattawa sun yi fatali da bukatar daukar mataki kan Sanata Ali Ndume. Hoto: Mohammed Ali Ndume.
Asali: Facebook

Sanata ya bukaci hukunta Ndume kan kalamansa

Sanata Cyril ya bukaci daukar mataki mai tsauri kan Ndume saboda jifan 'yan Majalisar da mummunar kalma, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin na zuwa ne bayan dakatar da Ndume daga mukamin mai tsawatarwa na Majalisar a yau Laraba 17 ga watan Yulin 2024, Pulse ta tattaro.

Yayin da shugaban Majalisar, Godswill Akpabio yake kokarin tura bukatar ga kwamitin ladabtarwa, sataoci sun yi tawaye kan lamarin.

Musabbabin dakatar da Ndume daga mukaminsa

An dakatar da Ndume saboda sukar gwamnatin Bola Tinubu wanda jam'iyyar APC ta turo takarda Majalisar domin daukar mataki a kansa.

Ndume ya ce ana shan wahala a Najeriya inda ya ce kwata-kwata shugaban kasa bai san ma halin da ake ciki ba.

Jam'iyyar a nuna rashin jin dadinta kan abin da Sanatan ya yi inda ta ce ba za ta lamunci haka ba

Kara karanta wannan

Abin da ya faru kafin sauke Sanata Ali Ndume daga matsayinsa a majalisar dattawa

APC mai mulki ta aika takarda Majalisar inda ta buƙaci Sanata Ali Ndume ya fice daga jam'iyyar ya koma duk jam'iyyar da ta kwanta masa a rai.

Majalisa ta magantu kan hukunta Ali Ndume

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba za ta hukunta Sanata Ali Ndume ba bayan kalamansa a kan Bola Tinubu.

Jami'in yada labaran, Sanata Yemi Adaramodu ya tabbatarwa yan jarida cewa babu zancen daukan mataki kan Sanatan.

Amma sai daga bisani aka samu akasin abin da Sanata Yemi Adaramodu ya sanarwa yan jarida a lokacin hirar da aka yi da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.