Abin da Ya Faru Kafin Sauke Sanata Ali Ndume Daga Matsayinsa a Majalisar Dattawa
- A yau Laraba ne majalisar dattawan Najeriya ta sanar da sauke Sanata Ali Ndume daga matsayin mai tsawatarwa
- Haka zalika jami'yyar APC ta bukaci Ali Ndume ya fice daga jami'yyar zuwa jami'yyar adawa da yaga dama a fadin Najeriya
- Sai dai kafin majalisar ta sauke Ali Ndume a yau an samu wani abu da ya faru kan cewa ko za a sauke shi daga matsayinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yau ne majalisar dattawan Najeriya ta sauke Sanata Ali Ndume daga matsayin mai tsawatarwa a majalisa.
Haka zalika jami'yyar APC mai rinjaye ta bayyana yadda alakarta za ta cigaba da kasancewa tare da Sanata Ali Ndume.
Kafin sauke Sanata Ali Ndume, jaridar Daily Trust ta yi hira da kakakin majalisar domin jin ko za su dauki mataki kan Sanatan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin dakatar da Ali Ndume
Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da Sanata Ali Ndume ne biyo bayan kalaman da ya yi a kan gwamnatin Tinubu.
Sanata Ali Ndume ya ce Najeriya ana shan wahala kuma shugaban kasa bai san ma halin da al'umma suke ciki ba wanda hakan ya bata ran fadar shugaban kasa.
Abin da ya faru kafin sauke Ndume
Bayan samun kishin kishin din cewa majlisa za ta dakatar da Ali Ndume an tuntubi jami'in yada labaran majalisar.
Jami'in yada labaran, Sanata Yemi Adaramodu ya tabbatar wa yan jarida cewa babu zancen daukan mataki kan Sanatan.
Amma sai daga bisani aka samu akasin abin da Sanata Yemi Adaramodu ya sanar da yan jarida a lokacin hirar da aka yi da shi.
A yanzu haka dai jami'yyar APC ta ba Sanata Ali Ndume umurni cewa ya fita daga tafiyarta bisa kalamansa a kan shugaban kasa.
Sanata ya caccaki Ali Ndume
A wani rahoton, kun ji cewa kalaman Sanata Ali Ndume kan halin yunwa da ake ciki a ƙasar nan ba su yi wa Sanata Sunday Karimi daɗi ba.
Sanatan ya caccaki Ali Ndume inda ya buƙaci da ya daina furta kalamai masu kaushi kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng