Babbar Kotu Ta Mayar da Mataimakin Gwamnan da Aka Tsige Kan Muƙaminsa
- Mataimakin gwamnan jihar Edo da aka tsige, Kwamared Philip Shaibu ya yi nasara a babbar kotun tarayya mai zama a Abuja
- Mai shari'a James Omotosho ya mayar da Shaibu kan kujerarsa ta mataimakin gwamnan Edo, ya ce majalisa ta saɓawa kundin tsarin mulki
- Sai dai majalisar dokokin jihar Edo ba ta gamsu da wannan hukuncin ba kuma tuni ta ɗaukaƙa ƙara zuwa kotun gaba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta mayar da Kwamared Philip Shaibu kan kujerar mataimakin gwamnan jihar Edo watanni kalilan bayan tsige shi.
Mai shari'a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ne ya yanke wannan hukuncin a zaman shari'ar yau Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024.
Kotu ta maido mataimakin gwamnan Edo
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Omotoso ya ce majalisar dokokin jihar Edo ta saɓawa tanade-tanaden doka wajen sauke mataimakin gwamnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, alkalin ya bayyana cewa matakin tsige Shaibu ya saɓawa tsarin kundin mulkin Najeriya.
Baya ga maido da Shaibu, kotun ta kuma bayar da umarnin a biya shi albashi da alawus alawus dinsa tun daga watan Afrilu zuwa yanzu.
Majalisar jihar Edo ta ɗaukaka ƙara
Sai dai a halin yanzu, majalisar dokokin jihar Edo ta ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci da babbar kotun tarayya ta yanke.
Majalisar ta kuma shigar da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin har sai ƙotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci a shari'ar da ke gabanta.
Hukuncin na yau Laraba ya zo ne kimanin watanni uku bayan ‘yan majalisar sun tsige Shaibu, mai shekaru 54 daga matsayin mataimakin gwamnan jihar Edo.
Alkalin ya umurci sufetan ƴan sanda, Kayode Egbetoku, ya bai Shuaibu dukkan tsaron da yake buƙata domin komawa bakin aiki har zuwa ƙarshen wa'adinsa, Daily Trust ta ruwaito.
Ɗan majalisa ya ki karban muƙamin APC
A wani rahoton kuma tsohon ɗan majalisar tarayya, Hon Pally Iriase ya yi fatali da naɗin da APC ta yi masa a matsayin 'dan kwamitin kamfe a Edo.
Iriase ya bayyana cewa babu wanda ya tuntuɓe shi gabanin sanya sunansa kuma tun da jimawa ya jingine harkokin siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng