Kansiloli Sun Taru Sun Tsige Shugaban Karamar Hukuma, Ana Zarginsa da Ta’asar Kudi

Kansiloli Sun Taru Sun Tsige Shugaban Karamar Hukuma, Ana Zarginsa da Ta’asar Kudi

  • Kansilolin karamar hukumar Egor a jihar Edo sun tsige shugaban karamar hukumar bayan kama shi da cushe a kasafin kudi
  • Sun bayyana yadda aka zabe su watanni goma da suka gabata amma har yanzu ba su da ofisoshi, shi kuwa yana fantamawarsa
  • Kansilolin sun yi zaman zartarwar ne inda suka kada kuri'ar rashin gamsuwar da salon mulkin shugaban tare da tsige shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Majalisar karamar hukuma ta tsige ciyaman din Egor dake jihar Edo, Hon. Eghe Ogbemudia kan zargin aringizo a kasafin kudin karamar hukumar tare da sauran zarge-zargen rashawa.

Wannan tsigewar na zuwa ne bayan kada kuri'a rashin gamsuwa da salon mulkin shugaban karamar hukumar a wani taron kansiloli da suka gudanar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunar hari a Zamfara, mutum 4 sun mutu yayin da aka sace 150

An tsige shugaban karamar hukuma kan zarge-zargen rashawa
Edo: Kansiloli sun tsige shugaban karamar hukuma aringizo a kasafin kudi. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Zaman tsige ciyaman din ya samu jagorancin shugaban majalisar karamar hukumar kuma kansila mai wakilar gunduma ta uku, Godwin Uwadiae Edigin, Channels TV ta bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edo: Kansiloli sun tsige ciyaman

An ce kansila mai wakiltar gunduma ta biyu, Hon. Stella Ogida ce ta mika bukatar kada kuri'ar rashin gamsuwa da mulkin shugaban karamar hukumar.

"Wannan ne wata na 10 bayan rantsar da mu amma mu kansilolin Egor ba mu da ofisoshi. Mun bankado aringizon kudi da aka yi a kasafin kudin mu da ya kai N1.7 biliyan.
"Shugaban karamar hukumar bai saka kansiloli yayin shirin da amincewa da kasafin kudin ba. La'akari da abubuwan da ke faruwa, ina son a kada kuri'ar rashin cancatar mulki.

- Inji Hon. Stella.

Ana zargin ciyaman da aringizo a kasafi

Yayin goyon bayan wannan kuduri, Hon. Elliot Inneh, kansila mai wakiltar gunduma ta tara ya ce:

Kara karanta wannan

"Muhimman cigaba 3 da za a gani bayan samun 'yanci" Inji Tsohon shugaban karamar hukuma

"Mun yi ta kokarin ganawa da shugaban karamar hukumar amma hakan ya gagara. A gabanmu a yau, muna da kasafin kudin da ya kai N6.054bn da aka amince da shi.
"Amma abun mamalin shi ne, mun gano cewa shugaban karamar hukumar tare da hadin guiwar wasu shugabannin, ya koma ta bayan fage ya kara N7.896bn a kasafin."

Shugaban zauren karamar majalisar, ya bukaci a kada kuri'a da baka, inda mafi rinjayen kansilolin suka amince da bukatar tsige shugaban karamar hukumar.

Karancin albashin da zan bada - Dan takarar gwamna

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa dan takarar gwamnan jihar Ondo, Ayodele Olorunfemi daga jam'iyyar LP, ya bayyana karancin albashin da zai biya ma'aikata idan aka zabe shi.

Olorunfemi yace zai gwangwaje ma'aikatan da Naira dubu dari da ashirin a matsayin sabon albashi matukar suka zabe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.