Hukumar Zabe Ta Sanar da Ranar Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Kaduna

Hukumar Zabe Ta Sanar da Ranar Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Kaduna

  • Hukumar zaɓe ta jihar Kaduna ta zaɓi ranar 19 ga watan Oktoba, 2024 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen kananan hukumomi
  • Shugabar hukumar KAD-SIECOM, Hajara Mohammed ta bayar da tabbacin cewa sun gama duk wasu shirye-shirye na zaɓen a wannan rana
  • Wannan na zuwa ne yayin da wa'adin ciyamomi da kansiloli da ke kan mulki yanzu zai ƙare ranar 31 ga watan Oktoba, 2024

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Hukumr zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta sanya ranar da za a gudanar da zaɓen kananan hukumomi a faɗin jihar.

Hukumar ta sanar da cewa ta shirya gudanar da zaɓen kananan hukumomin Kaduna a ranar 19 ga watan Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnoni 13 da suka fara gaggawar shirya zabe bayan hukuncin Kotun Ƙoli

Gwamna Uba Sani.
Hukumar KAD-SIECOM za ta gudanar da zaben kananan hukumomi ranar 19 ga watan Oktoba a Kaduna
Asali: Facebook

Shugabar KAD-SIECOM, Hajara Mohammed ce ta bayyana haka yayin ganawa da jam'iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki a Kaduna, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wa'adin ciyamomin Kaduna zai kare a 2024

Hajara Mohammed ta lura cewa ciyamomi da kansilolin da ke mulki yanzu sun shiga ofis ranar 1 ga watan Nuwamba, 2021 kuma wa'adinsu na shekara uku zai kare ranar 31 ga watan Oktoba, 2024.

Ta ƙara da cewa hukumar KAD-SIECOM ce take da alhakin shirya zaɓen shugabannin ƙanananan hukumomi, mataimakansu da kuma kansiloli.

"A bisa tanadin sashe na 25(1) na dokar KAD-SIECOM 2024, muna sanar da jama’a cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Kaduna ranar Asabar 19 ga Oktoba 2024 tsakanin karfe 8 na safe zuwa 4:00 na yamma," in ji ta.

Kaduna ta gama shirin zaɓen kananan hukumomi

Kara karanta wannan

Kotu ta tsige ɗan majalisar tarayya, ta umarci hukumar INEC ta shirya sabon zaɓe

An tattaro cewa hukumar ta fitar da jadawalin zaben tun a ranar Talata 16 ga Yuli, 2024.

Shugabar hukumar zaɓen Kaduna ta ci gaba da cewa an fitar da ka’idojin zaben ƙananan hukumomin tare da jadawalin zaben, rahoton Guardian.

Ta kuma bai wa bangarorin da abin ya shafa tabbacin cewa hukumar a shirye take ta gudanar da zaben a ranar da aka sanya.

Gwamnan Kaduna ya yi ta'aziyyar rasuwar Ekene

A wani rahoton kuma Malam Uba Sani ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalan Hon Ekene Abubakar Adams, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Chikun/Kajuru

Gwamna Uba Sani ya bayyana marigayin a matsayin ɗan siyasa mara tsoro wanda ya sadaukar da kansa wajen yi wa al'umma hidima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262