Gwamnan PDP Ya Hango Matsaloli a Ƴancin Kananan Hukumomin Najeriya
- Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya ce bai taɓa ɗaukar ko sisi daga kason kuɗin da ake turo ma kananan hukumomin jihar ba
- Fasto Umo Eno ya yi maraba da hukuncin kotun koli na bai wa kananan hukumomi cikakken ƴancin karbar kason kudinsu daga tarayya
- Ya ce matsalar da yake hangowa ita ce taya ciyamomi za su ɗauki nauyin biyan albashin ma'aikata a kan lokaci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa hukuncin kotun ƙoli na bai wa kananan hukumomin damar cin gashin kansu zai taimaki gwamnatinsa.
Gwamna Eno na jam'iyyar PDP ya ce bai taba ɗaukar ko sisi daga cikin haƙƙin ƙananan hukumomi 23 na jihar ba tun da ya hau kan madafun iko.
Umo Eno ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a filin jirgin sama na Uyo jim kaɗan bayan ya koma gida daga wata ziyarar aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, gwamnan ya yi maraba da hukuncin kotun kolin wanda ya ce wani ƙarin raguwar nauyi ne ga gwamnatocin jihohi.
Gwamna Eno ya hango matsaloli
Sai dai gwamnan ya nuna damuwa kan yadda shugabanni a matakin ƙananan hukumomin za su aiwatar da tsarin cin gashin kai da kotu ta ba su, Daily Post ta kawo.
Fasto Eno ya nuna danuwa musamman kan yadda jagororin ƙananan hukumomin za su tafiyar da wasu abubuwa da za su koma kansu kamar biyan albashin ma'aikata a kan kari.
"Kotun koli ta yanke hukunci, ita ce kotu mafi ƙololuwa a ƙasar nan, amma mu a nan Akwa Ibom ba na tunanin muna da wata matsala, a wuri na wannan hukuncin ya yi daidai.
"Kalubalen da nake hange wanda ya kamata mu zauna mu nemo hanyar da za mu bi, shi ne taya za a rika biyan ma’aikatan kananan hukumomi albashi a kan lokaci?
“Ta ya za a biya malaman firamare albashi a kan kari? Ta yaya za mu biya bashin da ke kanmu? Ina fatan zamu lalubo hanyar da za a kaucewa kowace matsala."
- Gwamna Umo Eno.
Gwamna Fubara ya jaddada goyon bayan Tinubu
A wani rahoton kuma Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara na jam'iyyar PDP ya tabbatar da goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Fubara ya kuma bukaci ƴan Najeriya su jingine duk wani banbanci da ke tsakani, su marawa gwamnatin tarayya baya don ta yi nasara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng