Rikici Ya Barke a PDP, Ana Neman Tumbuke Shugabar Jam’iyya
- Wasu matan PDP sun gudanar da zazzafan zanga zanga a birnin tarayya Abuja saboda rashin jin dadin wasu lamuran jami'yyar
- Jagorar mata masu zanga zangar, Dakta Obianuju Ogoko ta bayyana matsalolin da suke fuskanta a tafiyar mata a jami'yyar PDP
- Dakta Ogoko ta kuma bayyana matakin da suke bukata uwar jam'iyyar PDP ta dauka cikin gaggawa domin su cigaba da tafiya tare
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - Masu mata a jami'yyar PDP sun fusata har sun kai ga zanga zanga a hedikwatar jami'yyar a Abuja.
Matan sun gudanar da zanga zangar ne domin nuna kin amincewa da jagorancin shugabar matan jami'yyar ta kasa, Amina Darasimin D. Bryhm.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa masu zanga zangar sun bukaci uwar jami'yyar ta gaggauta dakatar da Amina Darasimin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin rikicin matan jam'iyyar PDP
Dakta Obianuju Ogoko ta bayyana cewa shugabar matar tana nuna musu halin da bai kamata ba a harkar shugabancin jam'iyyar.
Masu zanga zangar sun bayyana cewa an samu nuna wariya a jagorancin Amina Darasimin da wasu abubuwa marasa dadi.
Saboda haka suka ba uwar jami'yyar kwanaki uku su dakatar da ita daga jagoranci domin kawo cigaba a tafiyar matan PDP a Najeriya.
Martanin shugabar matan PDP
A nata bangaren, shugabar matan PDP ta kasa Amina Darasimin D. Bryhm ta ce lamarin ya zo mata da mamaki, rahoton Vanguard.
Ta bayyana cewa yawanci abubuwan da ake zarginta da su ba ta da alakar shugabanci da waɗanda suka aikatasu kwata kwata.
Amina Darasimin ta yi kira ga daukacin masu zanga zangar kan cewa su hada kai wajen ci gaba da tafiya tare da kawo ci gaba a PDP.
Rikicin jam'iyya: PDP ta ba 'ya'yanta hakuri
A wani rahoton, kun ji cewa Umar Damagum ya bayar da tabbacin cewa jam'iyyar PDP na shirin dawowa kan turbar nasara a babban zaɓen 2027 mai zuwa.
Muƙaddashin shugaban PDP ya bai wa 'yan jam'iyyar hakuri kan rikicin cikin gida, inda ya ce za su karɓe mulki daga hannun APC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng