Gwamnan PDP Ya Bayyana Goyon Bayansa ga Tinubu, Ya Faɗi Mafita a Najeriya
- Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara na jam'iyyar PDP ya tabbatar da goyon bayansa ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- Fubara ya kuma bukaci ƴan Najeriya su jingine duk wani banbanci da ke tsakani, su marawa gwamnatin tarayya baya don ta yi nasara
- Mai girma Fubara ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma kuma mai sarƙaƙiya wanda ke kunshe da al'umma masu banbancin al'adu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Siminialayi Fubara ya nuna goyon bayansa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan ya yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su marawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu baya domin ta samu nasara a manufofin da ta sa a gaba.
Fubara ya faɗi haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin majalisar wakilai karkashin jagorancin Chinedu Ogah a gidan gwamnati da ke Fatakwal ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Siminalayi Fubara ya godewa kwamitin bisa ziyarar da ya kawo jihar Ribas, inda ya ƙara da cewa yana fatan za su cimma nasara a abin da ya kawo su, The Nation ta ruwaito.
Gwamna Fubara ya hango mafita
"Ina miƙa godiya a gare ku musamman yadda kuka kawo mana ziyara. A madadin gwamnati da ɗaukacin al'ummar Ribas muna tabbatar maku da cewa kun ɗauko turba mai kyau.
"Kun yi abin da ya dace kuma ina da yaƙinin daga nan zuwa ƙarshen zamanku a nan, za ku lalubo mana hanyoyin da za su warware wasu daga cikin matsalolin mu.
"Amma a dunkule ya zama wajibi mu hada hannu waje guda mu marawa Shugaban kasar mu baya. Najeriya kasa ce babba mai sarkakiya, akidu da al'adu daban-daban, amma duk muna nan a matsayin daya saboda tutar Najeriya."
- Gwamna Simi Fubara
Fubara ya ƙara da cewa babban abin da ake buƙata shi ne kowa ya jingine batun banbanci, a haɗa hannu wuri ɗaya domin cimma manufa guda, Pulse ta ruwaito.
Tinubu zai miƙa kudirin albashi ga majalisa
A wani rahoton kuma, an ji shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ka iya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ga majalisar tarayya a makon gobe.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Muhammed Idris ne ya faɗi haka a Abuja, ya ce Tinubu zai gana da ƴan kwadago ranar Alhamis.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng