Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar Tarayya, Ta Umarci Hukumar INEC Ta Shirya Sabon Zaɓe
- Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓe a jihar Sakkwato ta soke nasarar wani dan majalisar wakilan tarayya Umar Yusuf Sabo
- Ta kuma umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta shirya sabon zaɓe a rumfunan zaɓe huɗu daga nan zuwa kwanaki 90
- INEC za ta janye shaidar lashe zaɓen da ta bai wa Umar kana ta shirya zaɓe a rumfunan da hukuncin ya shafa a Yabo da Shagari
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisa ta tsige ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Sabo da Shagari, Umar Yusuf Sabo.
Kotun ta kuma umarci Umar Sabo (Ɗanmaje) ya biya wanda ya shigar da ƙara N500,000 a matsayin ladan wahalar da shi.
Kotu ta soke zaben 'dan majalisa
Shugaban kwamitin alkalai uku na kotun mai shari'a Ashu A. Ewah ne ya karanto hukuncin, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana zaɓen da aka yi a mazaɓar Yabo/Shagari a matsayin wanda bai kammalu ba.
Sauran alkalan da suka yanke hukuncin sun haɗa da mai shari'a Helen N. Hamman Joda da mai shari'a Ali T. Changbo.
Dalilin soke nasarar Umar Yabo
Mai shari'a Ewah ya bayyana cewa zaɓen da INEC ta gudanar a 2023 da wanda ta ƙarasa a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2024 cike yake da magudi.
Sakamakon haka ya umarci hukumar zaɓen ta sake shirya ƙarishen zaɓe cikin watanni uku masu zuwa domin tantance sahihin ɗan majalisar Yabo da Shagari.
Wuraren da za a sake zaben majalisa
Jaridar Leadership ta tattaro cewa za a gudanar da sabon zaɓen a rumfuna huɗu a ƙananan hukumomin Yabo da Shagari.
Runfunan zaɓen sun hada da Dagawa Maji Kira, Dagawa Mai Zane, Shiyar Magaji, Kesoji Shiyar Hakimi, Jaredi Maji Kira, da Mazoji.
Bugu da kari, kotun ta umarci INEC da ta karɓe takardar shaidar cin zabe da ta ba Umar Yusuf Yabo.
APC ta buƙaci matasa su ƙara hakuri
A wani rahoton kuma jam'iyyar APC mai mulki ta yi kira na musamman ga daukacin matasan Najeriya su dakatar da shirye-shiryen gudanar da zanga zanga.
Har ila yau, APC ta bayyana matakan da 'ya'yan jami'yyar ya kamata su dauka domin ganin ba a samu nasarar zanga zangar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng