Gwamnoni 3 Na Cikin Matsala, Ganduje Ya Jero Jihohin da APC Za Ta Ƙwace a 2027

Gwamnoni 3 Na Cikin Matsala, Ganduje Ya Jero Jihohin da APC Za Ta Ƙwace a 2027

  • Shugaban APC na ƙasa ya tarbi tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki
  • Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta samu ƙwarin guiwar kwace mulkin jihohi uku a Kudu maso Gabas a zaɓen 2027
  • Mataimakin shugaban APC na shiyyar ya ce sun gama tattaunawa da ƴan majalisar tarayya hudu da za su sauya sheka a Enugu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ebonyi - Shugaban APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar ta samu ƙofar da za ta kwace mulkin wasu jihohi a Kudu maso gabashin Najeriya.

Ganduje ya ce sauya sheƙar tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim zuwa APC wata alama ce da ke nuna yadda wasu jihohi za su bar tsagin adawa.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Rock, an yi shirun minti 1 saboda mutuwar Jigo

Shugaban APC na kasa. Abdullahi Ganduje.
Ganduje ya tarbi tsohon shugaban majalisar dattawa zuwa jam'iyyar APC Hoto: OfficialAPCNig
Asali: Facebook

A cewarsa, Sanata Anyim babban jigo ne ba a jihar Ebonyi kaɗai ba, yana da tasiri a ƙasa baki ɗaya, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya bayyana haka ne a Abakaliki a taron masu ruwa da tsakin APC na Kudu maso Gabas wanda ya samu halartar jiga-jigan jam’iyya mai mulki.

APC ta kudiri aniyar karɓe jihohi 3

A jawabinsa, shugaban jam'iyya mai mulki ya ce ya zama wajibi su haɗa kai wuri ɗaya domin samun nasara a zaɓen jihohin Abia, Anambra da Enugu.

"Jihohin Anambra, Abia da Enugu sun zame mana barazana amma na ji daɗin yadda a yanzu muka shirya kuma mun kudiri aniyar kwato waɗannan jihohi," in ji Ganduje.

'Yan majalisa 4 za su koma APC

A nasa jawabin, mataimakin shugaban APC na kasa, Ijeoma Arodiogu, ya sha alwashin cewa jam'iyyarsu za ta kwace jihohin Abia da Enugu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Sukar Shugaba Tinubu ta jawo sanatan Arewa na fuskantar barazana a zaben 2027

Ya kuma bayyana cewa APC ta kammala tattaunawa da ‘yan majalisar wakilai hudu na Labour Party a jihar Enugu kuma sun amince za su canza sheka.

Arodiogu ya kuma ce jam’iyyar ta karbi manyan jiga-jigan adawa a jihar Abia ciki har da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Chinedu Orji, Leadership ta ruwaito.

APC ta rasa babban jigo a Kano

A wani rahoton kun ji cewa yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan sarautar Kano, jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta ranar Jumu'a.

Sanata Masud Doguwa ya jagoranci ɗumbin magoya bayansa daga APC sun koma PDP, ya ce gwamnatin Tinubu ba ta da alƙibla.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262